Coronavirus: Iran ta soke Sallar Juma'a saboda annoba

Iran ta soke gabatar da Sallar Juma'a a birnin Tehran da kuma wasu manyan biranen yankunan kasar 22 a karon farko cikin gomman shekaru, don takaita yaduwar cutar corona.

Kasar ta kuma takaita zirga-zirga kan hanyoyin zuwa manyan wuraren ibadar mabiya Shi'a a Qom, wajen da annobar Covid-19 ta fara bulla da kuma Mashhad.

Ma'aikatar Lafiya Ta Iran ta yi gargadi cewa yawan wadanda suka kamu da cutar zai karu nan da kwanaki masu zuwa.

A ranar Alhamis, an ruwaito cewa an samu masu dauke da cutar 245 da kuma wadanda suka mutu 26.

A yanzu haka Iran ce ta biyu a yawan wadanda suka mutu daga cutar bayan China.

Mataimakiyar shugaban kasar Iran a bangaren sha'anin mata Masoumeh Ebtekar, wacce ita ce macen da take da mafi girman mukami a gwamnatin kasar, ta zamo babbar jami'a da ta kamu da cutar a baya-bayan nan, bayan an tabbatar da hakan ranar Alhamis.

Wata kafar yada labarai ta intanet ta kasar ta ruwaito cewa Ms Ebtekar ta halarci wani taro ne da Shugaba Hassan Rouhani da kuma wasu ministoci, jim kadan kafin a tabbatar da kamuwar ta.

Sannan ana ganin yawancin mutanen da suka kamu da cutar a kasashe makwabtan Iran sun same ta ne daga can, kamar irin su Afghanistan da Bahrain da Iraki da Kuwait da Oman da kuma Pakistan.

Zuwa yanzu mutum 82,000 sun kamu da Covid-19 a fadin duniya, sannan mutum 2,800 sun mutu tun farkon annobar a karshen shekarar da ta gabata zuwa yanzu.

Dukkannin mace-mace sun faru ne a China ban da 57, sannan masu dauke da cutura ma sun fi yawa a can idan aka dauke 3,664.