Yadda hana zuwa Umrah ya shafi 'yan Najeriya

Matakin da Saudiyya ta dauka na dakatar da bayar da biza ga masu zuwa Umrah saboda tsoron shigar coronavirus kasar na kawo fargaba.

Saudiyya ta hana maniyyata daga kasashen da cutar ta bulla zuwa Umrah da kuma ziyara a biranen Makkah da Madinah.

Hakan ya sa ana fargabar dokar za ta iya kai wa lokacin aikin Hajjin da ake sa ran gudanarwa a watan Agusta.

A lokacin da aka samu annobar cutar Ebola a 2014, hukumomin Saudiyya sun hana maniyyata aikin Hajjin daga Guinea shiga kasarta.

Miliyoyin 'yan Najeriya kan je Saudiyya a duk shekara domin yin Umrah ko sauke farali. Ko yaya matakin na Saudiyya zai shafe su?

Wasu daga cikin masu shirin zuwa Umrah sun fara bayyana matsayinsu game da matakin, duk da cewa yanzu coronavirus ba ta bulla a Najeriya ba.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin wadanda suka riga suka biya kudin kujera sun fara tuntubar kamfanonin shirya tafiye-tafiyensu game da kudadensu.

Hadiza Tanimu shugabar wani kamfanin shirya tafiye-tafiye ne na 7twelve Travel Agency, ta ce, "Mutane sun aiko mana da sako a kan cewa yanzu me zai faru da kudin da suka riga suka biya?"

Ta ce cutar da ta sa Saudiyya dakatar da bayar da biza ta kawo raguwar tafiye-tafiye da harkokin kasuwanci zuwa kasashe tare da tilasta soke tafiye-tafiyen da suka tsara.

Ta ce suna fata za a shawo kan matsalar da ta shafi cutar nan da watan Ramadan, duk da cewa Najeriya ba ta cikin kasashen da dokar ta shafa.

''Mun ba su hakuri mun ce musu su dakata kar su ta da hankalinsu, in sha Allahu tafiya za ta yiwu.''

Wasu daga cikin maniyyatan sun nuna fahimta game da matakin da kokarin da kamfanonin ke yi domin ganin sun samu zuwa Saudiyya domin gudanar da ayyukansu na ibada.

Coronavirus a Afirka

Coronavirus ta bulla a wasu kasashe Afirka inda ake ganin kasashen nahiyar ba su yi kyakkyawan shirin tunkarar cutar ba.

Amma Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce ta fara shirye-shirye domin tunkari yiwuwar bullar cutar.

Gabanin sanarwar Saudiyyar na ranar Laraba, NCDC ta ce babu cutar a Najeriya, bayan an zargi wani mutum da alamominta.

A sanarwar da ta fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce ba a samu alamun kwayar coronavirus ba a gwajin da aka yi kan wani mutumin.

Manyan kasashen Musulunci

Kasar Paikstan na daga cikin kasashen da dokar ta shafa, kuma 'yan kasar na daga kashen da suka fi zuwa aikin Hajji da Umrah a duk shekara, bayan Indonesiya da Indiya.

Sai dai hakan bai zo da mamaki ba. 'Yan Pakistan miliyan 2.1 ne suka yi Umraha a 2019, bayan miliyan 1.7 da suka yi ibadar a 2018.

Wane tasiri hanin zai yi?

Gwamnatin Saudiyya ta ce dakatar da bayar da bizar shiga kasarta ta wucin gadi ce, ko da yake har yanzu ba a samu bullar cutar a kasar ba.

Matakin ya sanya damuwa a zukatan maniyyata Umara da masu ziyara, saboda gwamnatin kasar ba ta fayyace tsawon lokacin dakatarwar da ta yi ba.

Musulmi kimanin miliyan takwas ne ke zuwa Saudiyya a duk shekara domin yin Umrah, yawancinsu a cikin watan Ramadan da lokacin aikin Hajji.

Coronavirus a Gabas Ta Tsakiya

Iran ta haramta wa masu dauke da coronavirus yin tafiye-tafiye a kasar. A ranar Alhamis gwamnatin kasar ta sanar da karuwar wadanda cutar ta kashe zuwa mutum 26.

A Kuwait kuma Ma'aikatar Lafiya ta ce mutum 43 da suka dawo kasar daga Iran sun kamu da cutar coronavirus.

Wani mutum na shida ya kamu da coronavirus a Iraki bayan dawowarsa daga Iran. Gwamnatin Iraki ta kuma haramta shiga ko fita daga yankunan da aka fi samun cutar.

Hukumomi a Lebanon kuma sun ce an samu mutum na biyu da ke dauke da cutar bayan ya dawo daga Iran.

A Bahrain kuma an dakatar da zirga-zirgar jirage zuwa Iraki da Lebanon, zuwa na gaba.

Zuwa yanzu 33 ne suka kamu da cutar a Bahrain bayan samun karin wasu mutum bakwai a ranar Laraba.

Gwamnatin Qatar kuma ta bayar da umurnin kwashe 'yan kasarta da 'yan kasar Kuwait daga Iran.