Sojan Najeriya ya kashe kansa da abokan aikinsa hudu

Wani sojan Najeriya da ke aiki da Rundunar Lafiya Dole wacce ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, ya kashe abokan aikinsa hudu, sannan ya harbe kansa.

Wata sanarwa da mukaddashin kakakin rundunar sojin kasar, Kanar Sagir Musa, ya aike wa manema labarai ranar Laraba da almuru ta ce sojan, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya kuma jikkata wasu abokan aikin nasa biyu.

"Wani Kofur din sojan Najeriya da ke aiki da Rundunar Lafiya Dole a Malam Fatori, ya rika harbin kan mai-uwa-da-wabi ranar 26 ga watan Fabrairun 2020 inda ya bude wuta kan abokan aikinsa hudu sannan daga bisani ya kashe kansa.

"Ya jikkata biyu daga cikin abokan aikin nasa amma yanzu suna wani asibitin Maiduguri inda suke jinya", a cewar Sagir Musa.

Ya kara da cewa rundunar sojin tana kokarin tuntubar iyalan sojojin da aka kashe.

A cewar Kanar Musa, rundunar sojin Najeriya ta fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano abin da ya haddasa shi.

Sojojin Najeriya dai na aiki tukuru wajen yaki da Boko Haram, inda masana harkokin lafiya ke cewa hakan yana shafar yanayin tunaninsu da lafiyar kwakwalwarsu.