An samu gawar wani matashi a kejin zaki a Pakistan

An tsinci gawar wani saurayi a cikin kejin zaki a gidan namun daji da ke birnin Lahore na kasar Pakistan.

Ma'aikatan Gidan Zoo din sun tsinci kokon kan mutum da kasusuwa da yagaggun kayan mamacin Muhammad Bilal, washe garin ranar da ya bace.

Hukumomin kasar na bincike domin gano musabbabin mutuwarsa da yadda aka yi har ya shiga kejin zakin.

Mazauna yankin na zargin sakacin ma'aikatan gidan namun dajin da haddasa mutuwar saurayin mai shekara 17.

A farkon makon nan ne aka kai wani samame a ofisoshin Gidan Zoo na Lahore Safari, wanda shi ne mafi dadewa a kasar.

Daraktan Gidan Zoo din Chaudhry Shafqat, ya ce a ranar Talata ne mutanen garin da ke makwabtaka da su suka nemi a taimaka musu neman saurayin.

''Mun ce musu dare ya yi sosai kuma akwai hadari a shiga neman wanda ya bacen a cikin duhu,'' in ji Mista Shafqat.

Yayin neman Muhammad ne ma'aikata suka gano wani kokon kan mutum da kasusuwa da wasu yagaggun kaya da 'yan'uwan Muhammad suka ce nasa ne.

Jami'ai sun ce dangin Muhammad sun shaida musu cewa ya bar gida ne tun ranar Talata da rana domin samo ciyawar dabbobi.

An tafi da gawar Muhammad zuwa asibiti don gudanar da gwaji domin gano hakikanin musabbabin mutuwarsa.