Shin matakin Ganduje na hana bara a Kano zai yi aiki?

    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

Yawan yin bara da almajirai ke yi a arewacin Najeriya ba sabon abu ba ne, domin gwamnatoci da dama a Najeriya musamman a arewacin kasar sun sha yin dokoki domin hana bara, sai dai abin ya faskara.

Domin kuwa dokar na kasancewa ne tamkar dokar sarki, wadda Hausawa ke cewa ba ta wuce kwana biyu.

Sai dai a wannan karon, gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya fito karara ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi hannun riga da mabarata a jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa makasudinta na hana barar shi ne tabbatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta kuma dole ga 'yan firamare da sakandare a fadin jihar.

Gwamnan kuma ya ce daga yanzu dole ne makarantun allo su shigar da darussan Turanci da Lissafi cikin tsarin koyarwarsu.

Sai dai tuni majalisar malaman jihar, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Khalil, ta ce akwai bukatar gwamnati ta tantance yawan almajiran da kuma samun hadin kan al'umma kafin ta dauki irin wannan mataki.

A cewar Sheikh Khalil: "Mu abin da muke cewa shi ne idan ana so a yi maganin bara ya kamata a samu hadin gwiwa tsakanin gwamnati da malaman addini da attaira da kuma makwabta, misali Bauchi, Jigawa, Katsina da Kaduna da Gombe da Jamhuriyar Nijar."

Ya kara da cewa suna goyon bayan matakin amma akwai gyare-gyare da yawa da suka kamata a gudanar kafin a aiwatar da shirin.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin wannan sabon tsarin da Ganduje ya bullo da shi tsari ne mai kyau, kuma idan aka bi wasu hanyoyi abin zai dore.

Dakta Bala Muhammad, malami ne a jami'ar Bayero da ke Kano kuma mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullum, ya bayyana cewa an dade ana kokarin aiwatar da wannan doka a jihar Kano sai dai abin ya gagara.

Ya bayyana cewa idan wannan dokar ta dore a jihar Kano, tabbas sauran jihohi ma za su bi sahun jihar domin dabbaka wannan dokar.

Ya kara da cewa ko a kwanakin baya sai da gwamnatin jihar ta ce akwai kusan almajirai miliyan uku da ke bara a kwaryar birnin Kano.

Sai dai ya bayyana cewa yana fata wannan tsari da gwamnatin ta dauko ya dore, domin ya ce ''ba ka shan alwashi da harkar gwamnati, domin harkar gwamnati daban take da sabanin hankali''.

Amma ya ce duba da wasu manufofi guda uku da suke kasa a yanzu da gwamnatin jihar ta fito da su, idan aka dore wajen amfani da su, za a samu nasara.

Manufofin sun hada da shirin ilimi kyauta kuma dole, da kuma manufar gwamnatin tarayya ta ciyar da yara 'yan firamare da sakandare.

Akwai kuma wani shiri da hukumar kula da ilimi a matakin farko ta UBEC na SBMC, wato School Based Management Committee, wanda shiri ne na kula da makarantu da kuma bayar da kudin gyara makarantu kamar yadda Dakta Bala ya shaida.

Ko a lokacin can baya da aka yi irin wadannan dokoki a jihohin Najeriya, a kan samu wasu malaman tsangayu na sukar batun hana bara inda suke cewa an saka wa almajirai ido.

A nasa bangaren, Dakta Bala ya bayyana cewa abin da yasa barar da almajirai suke yi ta zama abin sa ido, saboda halin ko in kula da ake nuna musu, ya ce ana barinsu cikin wani hali na ''rashin uba da uwa da rashin tsafta da rashin lafiya.

''Ba almajiranci za a hana ba, bara za a hana.'' Ya ce ''da a ce makarantu na da makewayi da abincin da yara za su ci, madalla duk da babu matsala''.

Sai dai Dakta Bala ya shaida cewa, domin ganin dorewar wannan shirin ya kamata gwamnatin jihar ta bude wani asusu na musamman wanda jama'ar gari da masu hannu da shuni za su rinka tallafawa.

Ya ce wadannan kudin da za a tara za a rinka amfani da su wajen ciyarwa da kuma lura da tsangayun.