Tsohon Shugaban Masar Hosni Mubarak ya rasu

Asalin hoton, Reuters
Tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya rasu yana da shekara 91.
Mubarak, wanda aka tumbuke daga kan mulki a 2011, ya rasu a wani asibiti da ke birnin Alkahira.
Mubarak ya shafe shekara 30 a kan mulki kafin juyin juya halin kasar Masar.
An same shi da laifi a kisan masu zanga-zanga yayin juiyin juya halin. A watan Maris din 2017 ne aka sauya hukuncin tare da sakin sa.
A ranar Talata ne gidan talbijin na kasar ya sanar da mutuwarsa. Amma tun kafin sannan da safiyar Talatar kafar yada labaran intanet ta Al-Watan ta sanar da mutuwar tasa a wani asibitin sojoji.
A karshen watan Janairu ne aka yi wa Mubarak tiyata. A ranar Asabar din da ta gabata ne dansa Alaa ya ce yana bangaren kula ta musamman a asibitin.
Mubarak wanda aka haifa a shekarar 1928, ya shiga rundunar sojin sama yana matashi kuma ya taka muhimmiyar rawa a yakin da aka yi tsakanin Ira'ila da kasashen Larabawa a shekarar 1973.
Ya zama shugaban kasa shekara biyar bayan nan, sakamakon kashe Shugaba Anwar Sadat da aka yi.
Ya taka muhimmiyar rawa a sasantawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
Amma duk da irin biliyoyin dalolin da Amurka ta samu na taimako a lokacin mulkinsa, rashin aikin yi da talauci da cin hanci sun ci gaba da samun wajen zama a kasar.
An fara samun tashe-tashen hankula a watan Janairun 2011, bayan da kasar ta bi sahun Tunusiya wajen yin zanga-zangar da ta hambarar da shugaban kasarsu.
Bayan an shafe kwana 18 ana rikici a Masar, sai aka tursasawa Hosni Mubarak suka daga mulki.











