Anchor Borrowers: Manoma sun zata tallafin Buhari kyauta ne

- Marubuci, Daga Awwal Ahmad Janyau
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
Kebbi na daya daga cikin jihohin da aka fi noman shinkafa a Najeriya inda Allah ya wadata jihar da yanayi na wurin da ya dace da noman rani wanda aka dade ana yi a jihar.
Kuma yadda gwamnatin tarayya ta ce ta mayar da hankali ga bunkasa sha'anin noma, yasa mutane da dama suka rungumi noman musamman na shinkafa.
A shekarar 2015 ne Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin tallafa wa kananan manoma da bashi da ake kira Anchor Borrowers domin bunkasa noma.
Kusan Naira biliyan 54 gwamnatin Najeriya ta ware wa shirin na Babban Bankin kasar. Kuma manoma da dama ne suka ce ya sauya rayuwarsu.
Shirin ya shafi bayar da tallafii ga kananan manoma musamman kayan noma na injunan ban ruwa da iri da takin zamini.
Sannan haramta shigo da shinkafa da gwamnatin Buhari ta yi ya kara zaburar da manoma rungumar noman shinkafa.
Bunkasar noma a Kebbi
Kimanin mutum dubu 100 ne hukumomi a jihar Kebbi suka ce sun amfana da tallafin bashin da ake ba kananan manoma karkashin shirin Anchor Borrowers.
Abdullahi Sai'du Argungu Maigandu mamba a kwamitin Anchor Borrowars na gwamnatin Kebbi ya shaida wa BBC cewa arzikin da ake samu yanzu ya lunka na baya kafin zuwan Anchor Borrowars.
"Kafin Anchor Borrowers manomi na samun tan uku zuwa hudu a kadada, amma yanzu manomi na samun tan takwas zuwa tara a kadada."
Kungiyar manoman shinkafa ta jihar Kebbi ta ce sama da tan miliyan uku ake samarwa na shinkafa duk shekara a jihar bayan shigowar Anchor Borrowers.
Shugaban kungiyar manoman shinkafar Muhammadu Sahabi Augie ya shaida wa BBC cewa duk shekara adadin karuwa yake na shinkafar da ake samarwa a jihar Kebbi.
Wani manomin shinkafa a Argungu Sani Sa'adu Wangarawa ya ce ya samu arziki bayan samun tallafin na Babban Bankin Najeriya, yayin da kuma wasu manoman suka ce tallafin da aka ba su bai taka kara ya karya ba.
Shehu Jaji Illelar Yari, wani manomi a Birnin Kebbi ya ce naira dubu 70 kawai aka ba shi a matsayin tallafi ba tare da samun taimakon sauran kayayyakin da ake bayar wa ba karkashin shirin Anchor Borrowers.
Manoma ba su fahimci bashi ba ne
Duk da shirin Anchor Borrowers ya yi tasiri ga rayuwar manoma amma shirin na fuskantar kalubale inda da dama daga manoman ba su fahimci cewa bashi ne aka ba su.
Manufar shirin shi ne taimakawa manoma da bashin kudi da kayan aiki, idan sun samu amfanin gona su biya bashin da aka taimaka masu da shi.
Amma rashin biyan bashin da aka ba manoman shi ne babban kalubalen da shirin ke fuskanta.
Wasu manoman sun zata tallafi ne kyauta daga Shugaba Buhari inda wasunsu suka ce ba su taba kai ko kobo da sunan biyan bashin ba.
Kungiyar manoman shinkafa reshen jihar Kebbi ta ce kalubalen da ta ke fuskanta kenan, inda shugabanta ya ce an fara daukar matakin shari'a kan manoman da suka karbi bashin suka kasa biya.
"Da yawa daga manoma sun yi tunanin kalmar tallafi da ake cewa sun dauka kyauta ake nufi," in ji Sahabi Augieshugaban kungiyar manoma shinkafa na jihar Kebbi.
Ya ce rashin fahimtar tsarin da rashin biyan bashin shi ke kawo cikas ga manufar da ake son cimma.
Sharuddan bashin ga manomi

Anchor Borrowers tsari ne da ya shafi banki kuma yana da sharudda da dole sai manomi ya cika su kafin ya samu tallafin.
Dole sai manomi ya mallaki asusun banki da lambar BVN kuma ya kasance gonar manomi ta kai daga kadada daya zuwa biyar.
Kuma hukumomin da ke bayar da tallafin sun ce bashin na zuwa ne ta hanyar kungiya.
"Manoma za su hada kansu ne ta hanyar kungiya kuma za su samu tallafin idan sun cika sharudda," in ji Maigandu.
Tallafin bai kai ga wasu manoma ba
Kamar yadda wasu manoman suka ce tallafin da aka ba su bai taka kara ya karba, wasu kuma na cewa sun dade suna neman bashin amma ba su samu ba duk da cewa suna noman da gaske.
Wasu manoman sun yi zargin cewa ana sa siyasa a tsarin Anchor Borrowers sai masu kafa ake ba, zargin da kwamitin shirin na jihar Kebbi ya musanta.
Maigandu ya ce tallafin da ake ba manoma shi ne tallafin da ya kai N250,000 amma ba kudin baki daya ake ba manomi ba.
"Ana ba manomi kayan aiki da suk hada da iri da injinin ban-ruwa da maganin kwari na rabin kudin."
"Sai manomi ya cika sharuddan da aka gindaya da ka'idojin shirin kafin ya samu tallafin," in ji shi.
Ga ci gaban shirin da dorewarsa akwai bukatar kara wayar da kan manoma wadanda yawancinsu mutanen karkara ne.
Me ya sa shinkafa ke tsada?
Bunkasar noman shinkafa a jihar kebbi ne dai ya haifar da yawaitar kamfanonin sarrafa shinkafar da suka hada da manyan kamfanoni da kanana.
Kuma samuwarsu ya bude wa manoma kasuwa inda a nan take, abin da suka noma za su sayarwa kamfanonin da za su sarrafa su gyare su sa buhu kamar 'yar waje su sayar a sassan Najeriya har zuwa kasashe makwabta.
Sai dai duk da budewar kasuwar manoman shinkafa da masu sarrafa ta amma a jihar Kebbi kuka ake da tsadar farashinta a kasuwa.
Wasu mutanen jihar Kebbi na mamakin yadda duk da noman shinkafar da ake amma kuma har yanzu farashinta na tsada.
"A nan jihar Kebbi sai ka samu shinkafa 'yar waje ta fi wadda aka noma a nan sauki, farashin Labana ya kai N16,600 inda 'yar waje har N14,500 kana samunta" a cewar wani magidanci a Birnin Kebbi.
Amma duk da ana ganin bashin da ake bayarwa da ruwa ga manoma na yin tasiri ga noman shinkafa da ke sa ta yi tsada a kasuwa, amma manoman na ganin masu sarrafa shinkafar ne ke tsawwala farashinta.
Shugaban kungiyar manoma shinkafa reshen Kebbi ya ce akwai hanyoyi da dama da kamfanonin sarrafa shinkafar za su iya mayar da kudadensu daga amfanin da suka samu na shinkafar a lokacin sarrafawa.
Amma manyan kamfanonin sarrafa shinkafar a jihar Kebbi sun ce farashinsu ya dogara ne da yadda suka samu shinkafar da kuma wahalar da suka sha wajen sarrafa ta.
"Muna la'akari da yadda muka saye shinkafar da kuma kudin wuta da ruwa da biyan ma'aikata da wahalar sarrafata," kamar yadda Abdullahi Idiris Zuru babban manajan kamfanin Labana a jihar Kebbi ya shaida wa BBC.
Yadda dai shinkafa ta koma abincin mai kudi da talaka a Najeriya, ya kamata ace wadda ake nomawa a kasar ta yi saukin da za a yi gaggawar rungumarta hannu biyu bayan matakin da gwamnati ta dauka na haramta shigo da ta waje.
Akwai kuma bukatar kara daukar matakai na inganta noman musamman a jihar Kebbi da ake noman shinkafar rani da damana.










