Kashi 87 cikin 100 na matalautan Najeriya a Arewa suke - Bankin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto da Babban Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa kashi 87 cikin 100 na matalautan da ke Najeriya suna zaune ne a arewacin kasar.
Rahoton ya ce talauci a yankin kudu maso kudancin kasar ya yi gagarumar raguwa tsakanin 2011 da 2016.
A ranar Litinin ne Bankin Duniyar ya fitar da rahoton.
"Talaucin da ake fama da shi a arewacin kasar musamman a arewa maso yammaci yana ci gaba da karuwa.
''Kusan rabin matalautan mutane suna zaune ne a arewa maso yamma kuma kashi 87 na matalautan kasar na zaune ne a arewacin kasar," a cewar rahoton.
Rahoton ya kara da cewa: "Talaucin da ake fama da shi a kudancin kasar bai wuce kashi 12 cikin 100 ba inda ake samun bambanci tsakanin yankunan da ke kudancin kasar.
''An samu raguwar talauci a yankin tsakanin 2011-2016."
A yanzu dai kason yawan mataulatan da ke Najeriya ya zarce na Indiya, kamar yadda rahoton ya zayyana.











