Abin da ke janyo rikicin addini a Najeriya - Sarki Sanusi

Sarki Sanusi

Sarkin kano Mai martaba Sanusi Lamido Sanusi ya ce matsalar jahilci ce ke jawo rikice-rikicen addini a Najeriya tsakanin musulmai da kiristoci.

Sarki Sanusi wanda ya wakilci Sarkin Musulmin Najeriya a wani taron neman mafita kan rikice-rikicen addini a Najeriya, da ke gudana a birnin Abuja, ya ce a tarihin musulunci musulmai sun taba zuwa hijira wajen shugaban kiristoci a kasar habasha.

Shi ma a nasa jawabin, Rabaran Mathew Hassan Kuka ya ce ya yi kisan jama'ar da ake yi a Najeriya ya isa haka inda ya nemi da a hada hannu a tunkari gwamnati domin ta dakatar da hakan.

Sarki Sanusi ya kara da cewa yadda "ake yada labaran karya a kafaffen sadarwa na daga cikin abubuwan da suke kara ta'azzara rikice-rikicen addini."

Rikicin addini da kabilanci dai a Najeriya ya zama wani al'amari da ya kici ya ki cinyewa a kasar.