EFCC ta kama wanda Amurka ke zargi da zambar intanet

Asalin hoton, EFCC
Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati a Najeriya ta damke wani mutum da 'yan sandan Amurka ke nema bisa zargin zamba ta kafar intanet.
Sanarwar da EFCC ta fitar a ranar Litinin ta bayyana cewa ofishinta na garin Ilorin ne ya cafke Festus Akinyemi Abiona mai shekara 38, wanda ta yi wata takwas tana nema ruwa a jallo.
Jami'an hukumar sun kwakulo shi ne daga gidan buyansa a garin Arepo na jihar Ogun a ranar 6 ga watan Fabarairu.
A watan Yulin 2019 ne 'yan sandan FBI suka zargi Festus Akinyemi da tura sakon imel na zamba da suka kira Business Email Compromise (BEC) da sauran laifuka ta intanet.
"A watan Mayun 2016 FBI ta samu bayanai cewa wasu sun kutsa cikin asusun wani kamfanin inshora a Amurka, inda suka sace kudi kusan dala 2,500 (kusan naira 900,000)," FBI ta bayyana.
Ta kara da cewa: "Mutanen suna da alaka sosai da Abiona da kuma sauran abokan aikinsa da ke aikata zambar BEC."
Binciken EFCC ya nuna cewa wani da ya yi alaka da Abiona ne ya aikata zambar, kuma an gano miliyoyin naira a asusunsa na banki da kuma wasu imel din da ya yi amfani da su.
EFCC ta ce wanda ake zargin ya zuba dukkanin layukan wayarsa a masai da kuma katikansa na ATM lokacin da ya yi arba da jami'anta.
Ta ce har yanzu ba ya ba ta hadin kai a binciken da take yi amma nan gaba kadan za ta gurfanar da shi a gaban kotu.










