Yadda jami'an tsaro suka azabtar da ni - Shehu Sani

Bayanan bidiyo, Sanata Shehu Sani

Latsa hoton sama domin sauraron sanata Shehu Sani

Tsohon dan majisar dattawan Najeriya Sanata Shehu Sani ya fito bayan shafe mako hudu a tsare a hannun hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Hukumar ta gurfanar da Shehu Sani a gaban wata babbar kotun da ke zamanta a Abuja bisa zargin zamba cikin aminci na dala 25,000, inda kotun ta bayar da belinsa.

Shehu Sani ya musanta zargin da EFCC ke masa na karbar kudin daga hannun wani dillalin motoci.

Sharudan belin da kotun ta ba shi sun hada da biyan naira miliyan 10 sannan ya mika mata takardar fasfonsa.