AU: Shugabannin Afirka na tattaunawa kan yakin Libya

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Lahadi ne za a fara taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka , yayin da shugabannin kasashe daga fadin nahiyar suka taru a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
Kasashen Afrika 55 ne cikin kungiyar ta AU kuma wannan ne taronta na koli karo na 33.
Rikicin Libya ne babban jigon da za a tattauna a taron kuma shugabannin za su tattauna kan yadda za a kawo karshen yakin Libya da ya ki ci ya ki cinyewa.
Jigon taron na bana a hukumance shi ne 'Kawo karshen hare-haren bindiga, wanda ke nuni ga kawo karshen rikice-rikicen da suka addabi wasu kasashen nahiyar.
Haka kuma shugabannin na so ne su jagoranci shirin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru ana yi.
Taron zai duba matakan da za a bi don kare kasashen daga sabuwar cutar coronavirus, duk da cewa babu kasa ko daya a Afirka da ta samu bullar cutar.
Ana sa rai shugabannin kasashe za su halarci taron ciki har da Firayim Ministan Canada Justin Trudeau da Sakatare Janar na Maljalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.







