Buhari zai halarci taron AU a Habasha

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, TWITTER/MINISTRY_FOREIGN_AFFAIRS

Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je Habasha domin halartar taron koli na Kungiyar Tarayyar Afrika, AU, a Addis Ababa babban birnin kasar.

Mai taimaka wa shugaban kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa shugaban zai tafi ne a ranar Juma'a, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai hadu da takwarorinsa na sauran kasashe 55 da ke cikin kungiyar ta AU domin yin taronta na koli karo na 33.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Za a gudanar da taron shugabannin kasashen kungiyar ne a shelkwatarta da ke birnin Addis Ababa a ranakun 9 da 10 na wannan watan na Fabrairu.

Taron kolin ya kunshi kananan taruka daban-daban inda za a tattauna batutuwa da dama.

Jigon taron na bana shi ne 'Kawo karshen hare-haren bindiga: Samar da yanayi mai kyau don ci gaban Afirka.'

Wannan na nufin kokarin hana hare-haren bindiga wata dama ce ta tabbatar da shirin Aspirations of Africa's Agenda 2063, wanda ya mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro da kwnaciyar hankali a Afrika.

Tuni dai majalisar zartarwar kungiyar, wadda ta kunshi ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar suka soma ganawa a birnin na Addis Ababa a yau Alhamis.