AU ta bukaci a dakatar da sakamakon zaben DR Congo

Asalin hoton, EDUARDO SOTERAS
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta dakatar da fitar da sakamakon zaben shugabancin kasar na karshe.
Kungiyar da ke tabbatar da hadin-kai da demokradiya, ta ce tana da shaku sosai a kan sakamakon wucin-gadin da aka fitar a makon da ya gabata.
Dan takarar Jam'iyyar adawa Felix Tshisekedi aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaben, sai dai daya daga cikin abokan hamayyarsa, Martin Fayulu, ya dage a kan cewa shi ne ya yi nasara.
Kungiyar kasahen Afirka ta fitar da wannan sanarwar ne bayan taron da shugabaninta suka gudanar a birnin Addis Ababa na Habasha a kan zaben na Congo.
Shugabannin sun nuna damuwa da shakku a kan sahihancin sakamakon farko da hukumar zabe ta fitar.
A cewar sanarwar, Kungiyar na son gani an dakatar da fitar da sakamakon kamar yadda aka tsara a yau Juma'a.
Mista Fayulu ya zargi cewa Mista Tshisekedi da sakamakon wucin-gadi ke nuna cewa shi ne ya yi nasara ya kula yarjejeniya da shugaba mai barin gado Joseph Kabila.
Mista Kabila da ya shafe shekara 18 ya na mulki, tabbatar da wannan sakamako zai bada damar mika mulki irinsa na farko tun bayan samun 'yanci da kasar ta yi daga Belgium a 1960.
Hukumar zaben kasar ta ce, Mista Tshisekedi a yanzu na da kuri'u kashi 38.5 cikin 100, yayin da Mista Fayulu ke da kashi 34.7. Hadakar jam'iyyu da ke mulki da Emmanuel Shadary ke yi wa takara na da kashi 23.8 cikin 100.

Asalin hoton, Reuters
A ranar Asabar da ta gabata Mista Fayulu ya shigar da kara a gaban kotun kundin tsarin mulkin kasa, inda ya bukaci a sake kidaya kuri'un.
Sai dai wasu na ganin cewa ai akasarin alkalan kotun na da kusanci da jam'iyya mai mulki.
Ita ma dai Cocin Roman Katolika da ta tura mutum dubu 40 domin sa'ido a zaben ta nuna rashin gamsuwa da sakamakon.
Kwararu a kasahen Amurka da Faransa da kuma gwamnati Jamus, na diga ayar tambaya a kan sahihanci da gaskiyan zaben.











