Zabe a kasar Congo: Abubuwa biyar game da zaben shugaban kasar

Map of DR Congo over Western Europe
    • Marubuci, Alastair Leithead
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kasar congo - kasar da ta fi kowacce yawan arzikin ma'adanin Cobalt a duniya, wanda ake amfani dashi wajen hada wayar salula da motoci masu amfani da wutar lantarki - za ta yi zaben shugaban kasa a ranar Lahadi.

Mutane uku ne a kan gaba a kokarinsu na su gadar Shugaba Joseph Kabila.

Ga wasu abubuwa biyar game da kasar wadda saboda ma'adananta, ta ke da tasiri a tattalin arzikin duniya.

1) Ba a taba samun mika mulki a cikin lumana ba

Presentational white space

Tun samun 'yancin kai a 1960, sauyin mulki daga wani shugaba zuwa wani na zuwa da rikici.

Joseph Kasavubu ya zama shugaban kasa bayan zaben 1960, wanda aka yi wata daya kafin samun 'yancin kai kuma Patrice Lumumba ya zama Fira Minista.

Amma an cire Lumumba bayan rikicin neman mulki.

A 1961, cece kuce daga kasar da ta yayesu, Belgium, ya sanya aka kama shi inda aka mika shi ga 'yan tawaye inda suka kashe shi kuma suka narke kansa a cikin asid.

Mutum mafi karfi a lokacin shine Cif Mobutu Sese Seko, wanda ya zama shugaban kasa bayan ya yi juyin mulki a 1965.

An hambare Mobutu Sese Seko a 1997 bayan ya kwashe shekara 32 a kan mulki

Asalin hoton, Bettmann

Bayanan hoto, An hambare Mobutu Sese Seko a 1997 bayan ya kwashe shekara 32 a kan mulki

Bayan shekara 32 a kan mulki, an hambare shi a lokacin juyin juya hali tare da taimakon kashe makota da kuma juyin mulki.

Wanda ya gaje shi shugaban 'yan tawaye Laurent Kabila, mai gadinsa ne ya kashe shi a 2001.

Dansa Joseph Kabila ne ya gaje shi yana da shekara 29, shugaba mafi karancin shekaru a duniya a wancan lokacin.

Shekara biyu ke nan bayan lokacin da ya kamata ya sauka, Mr Kabila zai sauka a yanzu.

'Yan Congo da yawa suna fata a samu hannunta mulki a cikin lumana.

2) Kasa mai albarka

Kasar ita ce kashin bayan motoci masu amfani da wutar lantarki.

A cikin albarkatun kasar, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ke bada sama da rabin ma'adanin Cobalt - ma'adanin da ake amfani da shi wajen kera batirin motoci masu amfani da wutar lantarki dana waya.

A kiyasi, ya kamata a ce ma'adanan Cobalt da daiman da copper, zinari, sun sanya kasar Congo daya daga cikin kasashe mafi arziki a Afirka, amma mutanenta na daga cikin masu fama da talauci.

Kasar Congo ta sha fama da masu dibar arzikin kasar tun lokacin da turawa suka isa kasar a karni na 15.

A karni na 19, Sarkin Belgium Leopold na biyu ya tilasta mutane tattara masa roba domin hada taya, don biyan bukatar hada ma turawa keke da kuma mota.

Daga baya, Copper ta zama babban ma'adanin kasuwanci ga turawan mulkin-mallaka.

Bayan samun 'yancin kai, Mobutu ya samu kudade sosai inda kasar ta tsiyace.

A yanzu, rashawa da wulakantar da dukiyoyin al'umma ya sanya kasar gazawa wajen fidda mutanen daga talauci.

3) Babban wuri ne

Girman Jamhuriyar Demokradiyyar Congo kasa ce mai girman gaske.

Rashin abubuwan inganta rayuwa ya san wahalar zuwa wasu wurare, da kuma matsalolin kayan aiki a kan shirya zabe.

Hanyar kasar mafi girma ita ce ta Rafin Congo, kuma babu wasu manyan hanyoyi masu hada gabas da yamma.

Presentational white space

Gwamnatin kasar ta ki amincewa da taimakon majalisar Dinkin Duniya, wacce a da take da dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar na kimanin shekara 20.

Babban kalubale ne isar da abubuwan zabe ga mazabu 75,000 a kan lokaci.

4) Zabe ta hanyar Batir?

Sassa da yawa na Congo ba su da ruwan famfo da wutar lantarki, wannan abun damuwa ne idan aka yi zabe da injinan zabe.

Duk da cewa an yi amfani da su a wasu wuraren, wannan shi ne karo na farko da za ayi amfani da wadannan injinan a kasar.

Wannan ita ce na'urar da za a yi amfani da ita a zaben

Asalin hoton, Getty/JOHN WESSELS

Bayanan hoto, Wannan ita ce na'urar da za a yi amfani da ita a zaben

Kowanne mai yin zabe zai shiga wurin zabe domin zabar wanda yake so a kan wata na'ura mai kama da tebur.

Za a buga zabin nasa a kan takarda, sai mutum ya gabatar da shi.

Wadannan takardun ne za a kirga.

Sannan kuma na'urar za ta kirga kuri'un domin taimakawa wajen tabbatar da sakamakon.

Jam'iyyun adawa suna kokwanto a kan ko za a iya gudanar da sahihin zabe.

Akwai kuma damuwa a kan rashin hanyoyi masu kyau da karancin lokacin da aka kawo na'urori a kasar, watakila tsarin ba za ya wadata ba.

Matsalolin dai na da yawa, don kuwa kwana 10 kafin zaben wuta ta kama a inda ake aje na'urori zaben da aka ware wa Kinshasa inda sama da kashi biyu cikin uku suka kone.

5) Yaki da Ebola ya rikirkita kasar

Gabashin kasar Congo shine wurin da yaki yafi lalatawa a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Akwai kungiyoyin 'yan tawaye da yawa a kasar , amma kalubale mafi girma a yanzu shi ne a Beni dake kudancin Kivu.

'Yan Allied Democratic Forces (ADF) na kai hari ga mutane, dakarun kasar Congo, da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Har da wuraren dake da Ebola.

An tabbatar da barkewar cutar Ebola a wannan shekarar, kuma kimanin mutane 500 ne suka kamu da ita.

Presentational white space

Haduwar rashin zaman lafiya da kuma rashin amincewa da masu bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya, saboda hare-haren yan ADF duk da cewa akwai dakarun wanzar da zaman lafiya - na nufin cewa magance cutar zai yi wahala.

Wannan shi ne barkewar cutar karo na biyu mafi girma tun lokacin da aka gano cutar a Congo.

Sama da mutane 11,000 suka mutu a yammacin Afirka tsakanin 2013 zuwa 2016 - mafi yawanci a Laberiya, Guinea, da Saliyo.