INEC ta rage jam'iyyun siyasar Najeriya zuwa 18

Farfesa Mahmoud Yakubu

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da cewa ta mayar da jam'iyyun siyasar kasar zuwa 18 daga 92.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.

Farfesa Mahmaud ya ce INEC ta dauki matakin ne bisa damar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba ta na yiwa jam'iyyu rijista, da kuma soke rijastar jam'iyyu.

Ya ce hukumar ta yi duba kan irin rawar da jam'iyyun 92 suka taka a zaben 2019, da kuma zaaben cike gurbi.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shugaban na INEC yace nazarin da suka yi sun gano cewa jam'iyyu 16 ne suka cika ka'idojin da kundin tsarin mulki ya tanada na ci gaba da wanzuwa, yayin da jami'yyu suka gaza cimma ka'idar.

Ya kara da cewa daga daga cikin jam'iyyun Actions People Party APP ta garzaya kotu inda ta samu umarnin cewa kada INEC ta soke rijistar ta har sai kotun ta saurari karar da jam'iyyar ta shigar gabanta.

A cewar Farfesa Yakubu a yanzu APP za ta ci gaba da kasancewa jam'iyya har sai kotu ta yanke hukunci.

Jam'iyya cikon ta 18 ita ce Boot Party BP wacce aka kafa ta bayan samun umarnin kotu, abinda ke nan ya kai jam'iyyun zuwa 18.

"Don haka an soke rijistar 74," in ji Farfesa Mahmoud Yakubu.

Tuni dai hukumar ta zabe ta wallafa sunayen jam'iyyun da aka rushe da kuma wadanda ba a rushe ba.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2