Kwastam sun kama naira biliyan 2.8 a filin jirgin saman Lagos

Asalin hoton, FACEBOOK/NIGERIA CUSTOMS SERVICE
Hukumar yaki da fasa kauri ta Najeriya, ta ce ta kama dala 8,065,615 kwatankwacin naira biliyan 2.8 a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos.
Shugaban hukumar, Hameed Ali, ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ya gudanar ranar Talata a birnin Lagos.
Ya kara da cewa an kama kudin ne a cikin wata mota ana dab da shigar da kudin cikin wani jirgi.
Kakakin hukumar Mr Joseph Attah, ya shaida wa BBC cewa baya ga wadannan makudan kudi da aka kama, hukumar ta kuma kama karin wasu kudin.
Sau da dama hukumar tana kama makudan kudi a filayen jiragen saman kasar, galibi ana dab da sanya su a cikin jirgi.
Najeriya na cikin kasashen da cin hanci da rashawa da kuma safarar haramtattun kudi suka yi wa katutu.
Hameed Ali, ya ce an kama direban motar da ta dauko kudin da kuma wani jami'in hukumar NAHCO wadanda ake zargi da hannu a sama da fadi da kudin.
Ya ce, an kunshe kudin ne a cikin wata katuwar takarda mai ruwan kasa inda aka rubuta sunan mai kudin a bayan takardar.
Shugaban hukumar ta kwastam, ya ce tun da aka akam kudin, har yanzu ba bu wani banki da ya zo ya ce kudin na sa ne.











