Sojoji 'sun kama' wakilin jaridar Daily Trust a Borno

Asalin hoton, FACEBOOK/DAILY TRUST
Kamfanin Trust Media dake buga jaridar Daily Trust ya ce wasu sojoji sun kama wakilin jaridar a birni Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotanni sun ce sojojin daga runduna ta bakwai sun yi dirar mikiya a ofishin kungiyar 'yan jarida ta kasar da ke jihar ranar Alhamis suka yi awon gaba da Mr Olatunji Omirin da misalain karfe 4:40 na yamma.
Sojojin, wadanda biyu daga cikinsu ke sanye da kayan gida, daya kuma da kayan sarki rike da bindiga, sun saka wa Mr Olatunji Omirin ankwa a hannu sannan suka tafi da shi.
Babban editan jaridar Naziru Mikailu Abubakar ya tababbatar wa BBC lamarin.
Ya ce an shaida musu cewa tun da farko sai da sojojin suka fara zuwa ofishin jaridar Daily Trust na shiyyar, kafin su je ofishin kungiyar NUJ domin kama dan wakilin na su.
Editan ya ce suna yunkurin ganin an saki wakilin na su, sai dai ba su kai ga samun damar yin magana da shi ba.
Tuni kungiyar dake kare 'yan jaridu ta duniya ta yi Allah wadai da kamen da aka yi wa Olatunji Omirin.
Sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce ta kadu da yadda sojoji suka yi dirar mikiya suka kama Olatunji.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kamfanin Media Trust ya ce, Omirin ya shafe shekaru yana bayar da rahotanni kan ayyukan sojoji a Arewa maso gabas, musamman ma birnin Maiduguri.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake cika shekara daya da kwana 24 da wasu sojoji dauke da bindigogi suka yi wa ofishinsu na shiyyar Borno kawanya tare da yin gaba da babban mai kula da ofishinsu na Abuja, Uthman Abubakar da kuma wakilinsu, Ibrahim Sawab.











