Yarima Harry da Meghan sun ajiye mukamin gidan sarautar Burtaniya

Daga yanzu Harry da mai dakinsa Meghan ba za su sake amfani da mukamin sarautar Burtaniya ba.

Hakama yariman da matarsa ba za su sake karbar ko sisi ba daga kudaden al'ummar kasar.

Sanarwar da fadar Buckingham ta fitar ta kuma kara da cewa daga yanzu ma'auratan ba za su kara wakiltar Sarauniya ba a hukumance.

Da yammacin Asabar ne fadar da ke London ta sanar da hakan, bayan da Jikan na Sarauniya da mai dakin tasa suka bukaci da a sauke musu duk wani nauyi na mulkin al'umma da ya rataya ga wuyan masarautar don su samu damar tafiyar da rayuwa mai 'yan ci.

Babu tantama wannan mataki da Harry da Meghan su ka dauka bai yi wa masarautar Burtaniya dadi ba, to amma cikin sanyin jiki, Sarauniya ta bayyana cewa ta gamsu da dalilan ma'auratan kuma su da dan su Archie za su cigaba da zama 'yan gidan sarautar burtaniya har abada.

A yanzu dai sun yanke shawarar komawa Canada don gina sabuwar rayuwa da kudin aljihunsu.

To sai dai masana sun yi hasashen cewa ma'auratan sunyi gaggawar daukar wannan mataki wanda ya fusata al'ummar Burtaniya.

Kuma tun ba'aje ko'ina ba an bukaci Yariman da mai dakinsa da su biya zunzurutun kudi har fam miliyan 2.4 da suka sa aka kashe wurin yi wa gidan da suka zauna bayan aurensu kwaskwarima.

A cewar Buckingham palace gidan da ke Frogmore Cottage zai cigaba da zama masaukinsu a duk lokacin da suka ziyarci Burtaniya.

Wata tambaya da ke neman amsa itace sanin wanda zai dauki nauyin samar musu da cikakken tsaro a tsakanin Burtaniya da Kanada.

Da kuma yadda za su gudanar da rayuwa ta kashin kansu a wata kasa daban ba tare da sun tagayyara ba.

Ko a cikin jawabin da ta gabatar, Sarauniya Elizabeth ta ce 'ta fahimci irin kalubalen da suka ce suna fuskanta a baya bayan nan, kuma ta gamsu da matakin na su, amma fatanta shine ta ga cewa sun cimma burinsu a nan gaba.

Babban abinda ke da daure kai shine irin yadda masauratar da kuma gwamnatin Kanada su ka ki cewa komai game da wanda zai basu tsaron da ya dace.

A yanzu dai sarautar da suke rike da ita ta yarima da gimbiyar Sussex ta fita daga hannunsu, kuma kamar yadda Buckinghjam Palace ta sanar, ba za su kara amfani da sunan sarautar ba ko ina suka je a fadin duniya.

A bara ne Harry da Meghan su ka bayyana cewa an hana su sakat a Burtaniya musamman kafafen yada labarai da suka zarga da nuna wa Meghan wariya, kuma tun a lokacin ne suka bulguta shirin daukar wannan mataki.

Haka ma yarima Harry ya taba cewa yana fargabar matarsa za ta fada tarkon wadanda suka yi sanadin mutuwar mahaifiyarsa Gimbiya Diana.

Abunda aka zuba ido a gani shine irin kalar rayuwar da Harry da Meghan su ka shirya yi a Kanada, da kuma tasirin wannan mataki ga masarautar Burtaniya a shekaru masu zuwa.