Gimbiya Meghan ta koma Canada yayin da Sarauniya ke neman mafita

Gimbiyar Sussex ta koma Canada duk da tattaunawar da ake yi game da mukamin da za a ba ta ita da mai gidanta Yariman Sussex a nan gaba.

Ita da Yarima Harry sun kasance a Canada tun bayan bikin Kirsimeti tare da dansu Archie.

Hakan na zuwa ne yayin da Sarauniya da Yariman Wales da Duke na Cambridge suka tambayi ma'aikata su samar da maslaha bayan da Gimbiya Meghan da Yarima Harry suka sanar da kudirinsu na yin murabus daga matsayinsu na manya a fadar Birtaniya.

Fadar dai ba ta ji dadin matakin Harry da Meghan ba sai dai wasu majiyoyi daga fadar sun shaida wa BBC cewa Yarima Harry da Meghan ba su tuntubi kowa ba kafin fitar da sanarwar.

A sanarwar da suka fitar da yammacin ranar Laraba, Yarima Harry da Meghan sun bayyana kudirinsu na janyewa daga mukaminsu na manya a fadar tare da kokarin ganin sun tsaya da kafarsu.

Harry da Meghan sun shirya gudanar da harkokinsu tsakanin Birtaniya da arewacin Amurka yayin da kuma za su ci gaba da girmama Sarauniya.

Matakin ya zo ne "bayan watannin da suka shafe suna tattaunawa." a cewarsu.

A ranar Alhamis, rahotanni sun ce Sarauniya ta gana da Yariman Wales da Duke na Cambridge.

Sun kuma bukaci manyan ma'aikatan fadar da su yi aiki tare da iyalan Sussex da gwamnati domin samar da maslaha nan da 'yan kwanaki.

Daga bisani an tabbatar wa BBC cewa Meghan ta bar Canada.

Wasu rahotannin kuma na cewa sanarwar ta Harry da Meghan ta shammaci masarautar Buckingham.

Akwai tattaunawar da ake cikin masarautar game da makomar Meghan sai dai tattaunawar ba ta yi nisa ba.

Cikin wata sanarwa a ranar Laraba, masarautar Buckingham ta ce "Mun fahimci bukatarsu ta son daukar wata hanya ta daban amma akwai kalubale kuma za a iya daukan lokaci mai tsawo kafin a cimma matsaya."

Duk da matakin ma'auratan, Harry zai ci gaba da kasancewa mutum na shida a layin gadar mulki.

A watan Oktobar da ya gabata, Yarima Harry da Meghan sun fito sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta yadda kafafen yada labarai suka sa musu ido.

Bayan da suka koma Birtaniya bayan yin hutun tsawon mako shida a Canada a ranar Talata, Harry, mai shekara 35, da Meghan, mai shekara 38, sun ziyarci ofishin jakadancin Canada a Landan domin gode wa kasar bisa karbarsu inda kuma suka nuna jin dadinsu bisa yadda aka karbe su.

Tsohuwar mai yin fina-finai, Meghan wadda 'yar Amurka ce ta zauna tare da yin aiki a birnin Toronto, inda ta fito a wani shiri Suits kuma tana da kawaye da yawa 'yan Canada.