Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yarima Harry: Ba na son abin da ya faru da mahaifiyata Diana ya samu matata
Mai rike da sarautar Duke na Sussex na Burtaniya ya jaddada cewa "a ko da yaushe" zan kare iyalina, inda ya kara da cewa "ba zan yarda na shiga cikin yanayin da ya kai ga mutuwar mahaifiyata ba".
A lokacin da yake magana a wani shirin gidan talbijin na ITV, dan gidan saurautar ya ce ba ya son "a sake kwatawa".
Amma, mai dakinsa Duchess ta Sussex ta ce kawayenta na Burtaniya sun gargadeta da cewa kada ta auri yarima, saboda kafafen yada labarai za su yi matukar sanya ido a kanta.
Wani dan jaridar ITV, Tom Bradby ne ya yi hira da ma'auratan a lokacin da suke yin rangadi a Afrika ta Kudu a watan Satumba.
An tambayi Yarima Harry, mai shekara 35, ko yana fargabar cewa matarsa zata iya fuskantar matsin lamba daga kafafen yada labarai kamar yadda mahaifiyarsa Diane, Gimbiyar Wales, wadda ta mutu a wani hadarin mota a Paris a shekarar 1997 ta fuskanta.
Ya ce: "zan kare iyalina a ko da yaushe, musamman yanzu da nake da iyalin karewa.
"Don haka duk yanayin da ta shiga (Diana) da kuma abin da ya same ta, yana da matukar muhimmanci a kullum, duk kuwa da cewa ba wai ina fuskantar wata barazana ba ce a yanzu, amma dai bana son a sake kwatawa ne."
Bayan rahoton wata jarida a baya-bayan nan kan barakar da aka samu tsakanin masu sarautar Sussex da kuma Duke da Duchess na Cambridge, Yarima Harry ya ce shi da yayansa Yarima William, akwai ranakun " da suke dasawa" da kuma " wadanda ba ma dasawa".
Inda ya kara da cewa: "Wa da kani muke, kuma za mu ci gaba da kasancewa 'yan uwa.
"A halin yanzu dai kowa yana sabgar gabansa, amma a ko da yaushe ya ke da bukatata zan taimaka masa, kuma shi ma na san zai yi mini hakan a ko da yaushe."
Daga bisani yariman ya bayyana matsalar kwakwalwarsa da kuma yadda yake fuskantar matsalolin rayuwa na yau da kullum da cewa "abubuwan kulawa ne sosai".
Ya ce: "Na yi tsammanin duk wannan ta kau, amma sai kwatsam abu ya dawo sabo, don haka abu ne da ya zama dole na san yadda zan kula da shi.
"Wani bangare na wannan aikin shi ne na nuna baka damu ba, amma a gare ni da kuma matata akwai abubuwa da dama da ke kona mana rai, musamman ma saboda mafiya yawansu ba gaskiya ba ne.
Rangadin da suka yi na Afrika shi ne rangadin da yarima Harry da Meghan da kuma dansu Archie suka yi na farko a matsayin iyali a hukumance.
Duchess, wadda ta auri yarima Harry a Windsor Castle a watan Mayun shekarar 2018, kuma haihu a wannan shekarar ta yi magana a kan kasancewarta sabuwar 'yar gidan sarauta tun bayan aurenta.
Meghan tsohuwar tauraruwar fim wadda aka haifa a Amurka ta ce zama 'yar gidan sarauta ba abu ne mai sauki ba, inda ta kara da cewa sam bata shiryawa sa idon da jaridu ke yi mata ba.
"Lokacin da na hadu da mijina na yanzu kawayena sun yi murna domin ganin ina cikin farin ciki," In ji ta.
"Sai dai kawayena 'yan Burtaniya sun ce mini, 'Eh Mutumin kirki ne, amma kada ki aure shi don jaridun kasar za su lalata miki rayuwa. "
Meghan ta kuma gaya wa shirin talbijin din cewa ta yi "gwagwarmaya" da take da juna biyu da kuma bayan ta haihu, yayin da jaridu ke matukar sa ido a kanta.
An nuna shirin wanda aka kira Harry & Meghan: Ziyararsu zuwa Afrika, a gidan talbijin na ITV da yammacin ranar Lahadi a Burtaniya.
Bayan kammala rangadin nasu da kuma kammala nuna shirin, duke da duchess sun shigar da gidajen jaridu kara.
Meghan ta yi karar jaridar the Mail ranar Lahadi, bisa ikirarin cewa sun wallafa wasu wasikunta ba da amincewarta a hukumance ba.
Yarima Harry ya shigar da masu jarudun the Sun da News of the World da kuma Daily Mirrow kara gaban babbar kotu, bisa zarginsu da satar sauraron wayarsa, wani abin da ya faru sama da shekara goma da suka wuce.