Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a wannan makon

    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

Buhari ya saka hannu kan dokar kudi ta Finance Bill 2019

A yayin da hankalin kasar ya karkata kan Kotun Koli, a wani bangaren kuma Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar kudi, wadda za ta samar da hanyoyin aiwatar da kasafin kudin 2020, kamar yadda shugaban ya bayyana.

"Wannan ne karon farko tun bayan dawowar dimokuradiyya a Najeriya a 1999 da aka kaddamar da kasafin kudi tare da dokar aiwatar da shi a Najeriya," in ji Buhari.

Dokar mai suna Finance Bill, 2019, za ta taimaka wa masu manya da matsakaita da kananan san'o'i wurin yin kasuwancinsu cikin sauki.

Sannan kuma ta taimaka wa gwamnati wurin samun isassun kudi da kuma taimakawa wurin karfafa gwiwar masu zuba jari.

/

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Rashin lafiyar alkali ya kawo jinkiri ga hukuncin zaben gwamnoni

.

A ranar Litinin ne Kotun Kolin Najeriya ta daga zamanta da ta fara yi kan kararrakin shari'o'in zaben wasu jihohi da aka daukaka a gabanta,

Jihohin dai sun hada da Kano da Sokoto da Bauchi da Imo da Filato da Benue.

Jim kadan bayan kotun ta fara zamanta sai ta tafi hutu bayan ta fara da shari'a kan zaben Kano tsakanin dan takarar APC Abdullahi Umar Ganduje da kuma na PDP Abba Kabir Yusuf.

Bayan alkalan sun shafe sama da mintuna 45, sai suka aiko da cewa daya daga cikinsu ba shi da lafiya wanda hakan ya sa kotun da dage zamanta.

A wannan dalili ne ya sa kotun ta dage zamanta zuwa ranar Talata 14 ga watan Janairun 2020 wanda a wannan rana ce aka yanke hukunci kan zaben jihar Imo.

PDP ta yi martani kan hukuncin Kotun Koli

.

Asalin hoton, @EMEKAIHEDIOHA

Babbar Jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP ta ce ta yi mamakin hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Imo.

A ranar Talata ne Kotun Koli ta kwace kujerar gwamna daga Emeka Ihedioha na Jam'iyyar PDP ta ba Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sanarwar da kakakin jam'iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar bayan zartar da hukuncin ta ce, PDP ta kasa fahimtar dalilan da Kotun Koli ta yi dogaro da su na yanke hukuncin.

PDP ta kasa fahimtar yadda za a ce dan takarar da ya zo na hudu a zaben gwamna na 9 ga Maris da kuri'a 96,458 a ce ya doke dan takarar PDP da ya samu yawan kuri'u 276,404

A nata bangaren, jam'iyyar APC ta bayyana farin cikinta da hukuncin Kotun Kolin da ta bayyana dan takararta Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Imo.

APC ta ce duk da cewa ta yi mamakin yadda ta rasa kujerar gwamna a jihar Zamfara a Kotun Koli da kuma yadda kotun ta haramta mata shiga zabe a Rivers amma hakan bai sa ta cire tsammani ba ga kotun.

'Yan bindiga sun kashe mutum 29 a Zamfara

@BELLOMATAWALLE1

Asalin hoton, @BELLOMATAWALLE1

A wannan makon ne wasu 'yan bindiga suka afka kauyen Babban Rafi da ke karamar hukumar Gummi a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa mutum 29 maharan suka kashe, yayin da kuma sauran mutanen garin suka watse inda ya ce sun gudu zuwa wasu garuruwan jihar Kebbi.

"Sun ta bude wuta kuma ko wane mashin yana dauke da goyon mutum uku, suna bin mutane suna harbi suna kashewa, sun ci gari da yaki," in ji shi.

Rundunar 'Yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kai harin, amma kakakinta SP Mohammed Shehu ya shaida wa BBC cewa mutum 14 ne aka kashe, kuma ya ce maharan sun tsallako ne daga jihar Kebbi da ke makwabtaka da Zamfara.

An kai wa Sarkin Potiskum hari a Kaduna

.

Asalin hoton, Getty Images

A wannan makon ne mahara suka kai wa Sarkin Potiskum Alhaji Umaru Bubaram, hari inda suka kashe mutum shida, kamar yadda rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta bayyana.

Kakakin Rundunar 'Yan sanda a jihar Kaduna DSP Yakubu Abubakar Sabo ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.

DSP Sabo ya ce abin ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, a kusa da garin Marabar Jos da misalin karfe 11:00 na daren ranar Talata.

Ya ce wasu mahara ne suka bude wa ayarin motocin sarkin wuta wanda hakan ya yi ajalin mutum shida - biyu fasinjoji da ke tafiya a hanyar, hudu kuma daga cikin jama'ar sarkin.

Hakazalika ya ce tun farko 'yan bindigar ba sarkin suka hara ba.

Ya ce sun tare wata babbar mota ce dauke da fasinjoji da ke kan hanyarta ta zuwa Kaduna.

Ana cikin haka ne sai ga tawagar sarkin tare da jiniyar masu yi masa rakiya, abin da ya sa 'yan bindigar suka yi zaton jami'an tsaro ne kuma hakan ya sa suka fara bude wuta, in ji kakakin 'yan sandan.