Shin Iran za ta sake kai wa Amurka hari?

Mourners attend the burial of Qasem Soleimani

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Miliyoyin Iraniyawa ne suka fito domin binne Qasem Soleimani

La'akari da muhimmancin Janar Qaseim Soleimani, a iya cewa harin da Iran ta kai wa sansanonin sojin Amurka a Iraqi ya zama wani gagarumin martani.

Iran na ikirarin cewa ta illata dumbin dakarun Amurika, amma duk ba wannan ba ne abin damuwa ba. Amurka ta ce ta samu gargadin harin na Iran daga na'urorinta tun kafin kai harin a sansanonin da Amurka ta ce ba wani sojanta a wurin.

Abin tambaya a yanzu shi ne. Shin me zai faru a nan gaba, Shin wannan ne harin karshe na ramuwa na Iran? Lokaci ne kadai zai tabbatar.

Sai dai misali idan Iran ta yanke shawarar kashe wani babban jami'in Amurka a matsayin martani, abin zai dauki lokaci, kuma ya danganta da tsarin da ta yi da kuma lokacin da za ta samu damar aiwatar da aniyarta.

Dama can ta ce za ta mayar da martani, kuma martanin zai fito ne daga rundunar sojinta ba wai kungiyoyin da ke goya mata baya ba, kuma daga abin da ta yi na harba makamai masu linzami ranar Talata, ta cika alkawarin da ta yi kenan.

Ba shakka kalaman da suka fito daga dukkanin bangarorin sun nuna akwai alamar sassautuwar al'amura.

Sakon da shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter na cewa babu sojin Amurka ko daya da ya rasa ransa.

Da kuma martanin Iran da ke cewa ba zata sake kai wani hari ba face Amurka ta mayar da martani wanda hakan ya nuna an samar da kofar sulhuntawa, kuma dukkanin kasashen biyu na gudun aukawa yaki.

Don haka wannan lokaci ne da za a iya amfani da shi don dakile barazanar da ke akwai, duk da cewa Iran da Amurka ba za su sauya matsayarsu ta neman yin kaka-gida a gabas ta tsakiya ba.

Jim kadan bayan kai harin Farashin danyen mai ya tashi da kashi 1.4 cikin 100 inda ake sayar da ganga kusan dala 70.

Haka ma farashin zinari da darajar kudin Japan Yen sun tashi bayan da aka kai harin.

Kazalika hannun jari a duniya ya yi kasa sakamakon rikicin da ake yi a yankin gabas ta tsakiya.

Kafar talabijin ta Iran ta ce harin ramuwar gayya ce kan kisan Babban Kwamandan kasar Qasem Soleimani.

Harin ya faru ne sa'oi bayan jana'izar Soleimani wanda ya mutu sakamakon harin da jiragen Amurka mara matuka suka kai ranar Juma'a.

Mutuwarsa dai ta haifar da fargabar cewa rikici tsakanin Amurka da Iran na iya ta'azzara.