Iran ta kai hare-hare da makami mai linzami kan dakarun Amurka

Bayanan bidiyo, Bidiyon kafar yada labaran Iran da ke nuna yadda kasar ta kai harin makami mai linzami
Lokacin karatu: Minti 2

Akalla sansannin sojin Amurka biyu a Iraqi aka kai wa hare-haren makamai masu linzami, a cewar ma'aikatar tsaron Amurka.

Kafar yada labaran Iran ta ce harin na ramuwar gayya ne bayan kisan janar din soji kuma babban kwamandanta Qasem Soleimani da aka kashe a hari ta sama a Bagadaza, bisa umurnin shugaba Donald Trump.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce akalla sansani biyu aka kai wa hari a Irbil da Al Asad.

Babu dai wani cikakken bayani game da hare-haren na Iran.

Mai magana da yawun fadar White House Stephanie Grisham ta fadi cikin wata sanarwa cewa, "Mun samu rahotannin hare-hare kan sansanonin Amurka a Iraqi. An sanar da shugaban kasa kuma muna sa ido kan lamarin tare da tuntubar tawagarsa ta tsaron kasa,"

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta ce harin na ramuwar gayya ne kan kisan Soleimani a ranar juma'a

"Muna yin gargadi ga dukkanin aminnan Amurka, da suka bada sansani domin jibge dakarunta 'yan ta'adda, cewa duk wani yanki da aka fara kitsa hari kan Iran za a kai ma shi hari," kamar yadda kamfanin dillacin labaran Iran IRNA ya ruwaito.

Ministan harakokin wajen Iran Javad Zarif ya fitar da sanarwa a Twitter, yana cewa harin na kariyar kai ne tare da nesanta harin da nufin kara dagula al'amurra domin abkawa cikin yaki.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shugaba Trump shi ma ya wallafa a Twitter yana jaddada cewa "komi lafiya lau", inda ya kara da cewa ba su kai ga tantance ko an samu hasarar rayuka ba.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Presentational white space

An kai harin ne jim kadan bayan binne Soleimani. An kai hari na biyu Irbil bayan an kai na farko da makamin roka Al Asad, kamar yadda kafar Al Mayadeen ta ruwaito.

Tun da farko shugaba Trump ya ce janye dakarun Amurka zai kasance mataki mafi muni ga Amurka.

Kalamansa na zuwa bayan wata wasika da rundunar sojin Amurka ta ce an tura bisa kuskure ga Firaministan Iraqi, matakin da majalisar Iran ta amince kan bukatar janye dakarun na Amurka.

Amurka tana da yawan dakaru 5,000 a Iraqi.

Kisan Soleimani a ranar 3 ga Janairu ya kara tsamin dangantaka tsakanin Iran da Amurka.

Miliyoyin Iraniyawa ne suka fito kwansu da kwarkwata domin jana'izar babban kwamandan na Iran da Amurka ta kashe inda suke ta furta kalamai na barazana ga Amurka da kuma Trump

Akalla mutum 50 ne suka mutu yayin turmutsutsin jana'izar Soleimani.

Iran ta ce harin na ramuwar gayya ne kan kisan kwamandanta Qasem Soleimani

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Iran ta ce harin na ramuwar gayya ne kan kisan kwamandanta Qasem Soleimani