Ko kisan Soleimani zai bai wa Trump damar tazarce?

    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Corresponsal de la BBC en Washington DC

A bayyane take harin da Amurka ta kai wa babban kwamandan sojin kasar Iran, Janar Qasem Solemani, zai yi tasiri ga siyasar Shugaba Trump.

Kusan a iya cewa a yanzu komai da ke faruwa ana danganta shi da siyasa, haka kuma shi ne babban labari a ko'ina.

Yayin da wutar rikici ke kara ruruwa tsakanin kasashen Iran da Amurka, za a dauki dogon lokaci ba a warware ba, hasali ma ya danganta ne ga martanin da Iran ta maida kan kisan babban kwamandan nata wanda shi ne zai kara hasashen abin da zai faru nan gaba.

Idan har Amurka ta janye sojojin ta daga Iraki, siyasar da ke ciki za ta sake daukar dumi. Za a samu bangarori biyu, wato wadanda za su yi farin ciki har da shagali, yayin da daya bangaren za su yi kadaran-kadahan wato ba yabo ba fallasa.

A taikace wannan hari zai yi tasiri ta fuskoki da dama, haka kuma wannan zai shafi zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a yi a kasa da wata daya da kuma babban zabe da za ayi a watan Nuwambar bana.

Lokacin shugaba mai yaki?

Da ma bisa al'ada shugaban Amurka yakan fuskanci matsin lamba musamman idan na samun rikice-rikice daga kasashen waje, kuma dole a samu wani bangare da Amurka za ta karkata akai dan taimakawa.

Misali yakin yankin gabas ta tsakiya da aka yi a shekarar 1999, shugaban Amurka na lokacin George W Bush ya yi uwa da makarbiya a ciki.

Haka kuma George D Bush shi ma an ga irin rawar da ya taka da abin da ya biyo bayan harin 11 ga watan Satumba, da hare-haren da aka kai kasar Afghanistan.

Haka kuma shugaba Barack Obama bai ga wani sauyi ba kan amincewa Amurka ta kai hare-hare a lokacin da kasar Libya ta fada yaki a shekarar 2011.

A lokacin Shugaba Trump ya harba makamai masu linzami kasar Syria a matsayin martani kan amfani da makamai masu guba da gwamnatin shugaba Basharul Assad ta yi, hakan ya kara nuna karfin ikon da ya ke da shi da irin matakan da zai iya dauka kan wata kasa idan bukatar hakan ta taso.

Binciken farko da aka yi bayan harin da aka kai wa Qasem Soleimani, ya nuna Trump zai fuskanci kakkausar suka kan yadda ya tafiyar da lamarin.

Yayin da ya ke da ikon daukar matakin, akwai kuma matukar damuwa kan abin da hakan zai haifar tare da sukar shugaban ''bai yi kyakkyawan shiri da tuntuba kafin ya dauki matakin ba.''

An kai hari cikin kankanin lokaci, sojoji sun yi gagarumar nasara amma takaitacciya, an zubar da jini. To amma sakamakon ne har yanzu ake hasashen yadda za ta kaya idan har sai Iran ta maida martanin da ba a san wanne iri ne ba.

Goyan bayan jam'iyyar Republican

Shugaba Trump zai iya amfana da abin da ya faru, kamar yadda kullum ake masa kallon ya na yin galaba musamman kan irin kalamansa masu janyo cece-kuce.

Kamar yadda shafin intanet na Huffington Post da ke bibiyar yadda Amurkawa ke kallon shugaban, ya nuna kashi 83 cikin 100 na 'yan jam'iyyar Republican sun amince a kai hari ta saman kan tawagar Soleimani.

A bangare guda kuma magoya bayan shugaban suna kallon harin da aka kai ga Soleimani wata sabuwar hanya ce ta karfafa manufar siyasa da Trump ya yi amfani da ita.

A shafukan sada zumunta kuwa, duk wadanda ke goyon bayan Trump da ake ganin sun dan nuna damuwa kan abin da suke iya wallafawa shi ne ''sannu, lallai kun yi rashi.'' Wani shafin intanet mai suna Babylon ya wallafa wani shagube kan cewa jam'iyyar Democrat za ta sauke tutar Amurka kasa a matsayin alhini kan mutuwar Soleimani.

Idan muka je yankin gabas ta tsakiya, wani sabon abin kallo ne wanda zai karawa shugaban farin jini da dauke hankali kan shirin tsige shugaba Trump da 'yan majalisar dokokin Amurka ke yi.

Wannan shi ne kuma abin da shugaban ya tashi da shi, a ranar Litinin da safe tare da wallafawa a shafinsa na Twitter.

"Abin takaici ne yadda suka maida hankali kan gabar siyasa da bita da kulli, ni kuwa gani nan ayyuka ma sun yi min yawa.''

Wata dama ga Democrat

A bangaren jam'iyyar Democrat kuwa, harin da aka kai ya hallaka Soleimani zai kara musu wata dama ta kin goyon bayan masu neman rigima a cikin jam'iyyar da ba a kara jin bakin ta ba tun bayan yakin da aka yi a kasar Iraki.

Dan takarar shugaban kasa na gaba a jam'iyyar Democrat Bernie Sanders ya yi saurin yin jawabi kan aniyarsa ta son zaman lafiya.

''Abin da na fada a kan Vietnam gaskiya ne. Haka abin da na fada a kan Iraki shi ma gaskiya ne. Zan yi duk abin da ya dace da karfin ikon da nake da shi dan kaucewa yaki da kasar Iran,'' wannan shi ne sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ciki har da takaitaccen bidiyon da a ciki ya ke kokarin bayani kan kaucewa yaki. ''Babu wanda zan bai wa hakuri.''

Wata 'yar takara Tulsi Gabbard, ta bayyana karara ba ta ji dadin abin da ya faru ba inda suka ce "gwamnatoci sauya yaki suke yi", ta ce harin da aka kai wa Soleimani neman yin yaki ne da Iran, kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin Amurka.

Wadannan kalaman nata sun banbanta da na sauran 'yan takarar jam'iyyar Democrat, wadanda sukai allawadai da taimakon da Soleimani ke bayarwa dan yakar Amurka.

''Akwai tambayoyi mai tarin yawa kan yadda aka dauki matakin, sannan ko mun shiryawa abin da zai biyo baya,'' inji Pete Buttigieg. Yayin da Elizabeth Warren ta kira Soleimani da "mai kisan kai", ita kuwa Amy Klobuchar damuwa ta nuna kan makomar sojojin Amurka da yankin.

A bangare guda tsohon magajin garin New York Michael Bloomberg ya maida martani ne kan kalaman Sanders, inda ya ce ''abin takaici'' kuma bai da ce Sanatan ya kira harin da "kisa ne" kalmar da yawancin 'yan Democrat ke amfani da ita.

An samu rarrabuwar kawuna a dukkan jam'iyyar a kan shirin kiwon lafiya a lokacin da akai muhawara tsakanin 'yan takarar shugaban kasa. Idan rikicin Iran ya kara zafafa, amfani da karfin soji ka iya kasancewa wani batu da za a kara samun rabuwar kawuna tsakanin 'yan takarar.

Kalubale ga Biden

Kididdigar Huffpost poll kan harin da ya hallaka Soleimani wani daddadan labari ne ga dan takarar shugaban kasa Joe Biden, inda kashi 62 cikin 100 na 'yan Democrat da masu mara musu baya suka nuna sun yadda da shi idan ana batun kasar Iran. Yayin da Warren da Sanders kuma suka samu kashi 47 cikin 100 suka nuna amincewa da su duk dai kan batun.

Ba wani abin mamaki bane ka samu irin wannan sakamakon, saboda kowa da yadda yake kallon abubuwan da suka shafi siyasar kasashen waje.

Idan aka yi waiwaye za mu ga yadda Biden ya ja hankalin yankin gabas ta tsakiya na nuna goyon baya a yakin da aka yi a kasar Iraki a shekarar 2003.

Da yake bai wa wani mutum amsar tambayar da yayi a ranar Asabar a Iowa, Biden ya ce duk da ya kada kuri'ar amincewa da yakin da aka yi a kasar Iraki a bangare guda kuma ya soki lamirin Shugaba Bush kan yadda ya tafiyar da yaki tun da fari.

Biden dai ya bayyana goyon baya karara kan yakin tun da aka fara, a bangare guda kuma ya bayyana yin danasani da amincewar a shekarar 2005.

A duk lokacin da Biden ya wallafa goyon bayan yakin Iraki a shafinsa na Twitter, su kuma ma'abota shafukan sada zumunta sai su yi ca akan shi, tare da juya batun zuwa wata fuskar ta yadda hankali zai kara raja'a a kai.

Tsige Trump bai yi tasiri ba

Tamkar yunkurin tsige Shugaba Trump da aka fara a watan Disambar bara bai yi wani tasiri ba, idan aka yi la'akari da yadda ake ci gaba da samun tuttudowar manyan labarai da dumi-duminsu a Amurka, a yanzu kasar Iran za ta shiga takara da 'yan majalisar dokokin Amurka kan tsige Mista Trump ta amfani da irin martanin da za ta maida kan kisan Janar Soleimani.

Sai dai ba labari ne mai dadi ba ga kananan 'yan takara kamar Cory Booker, da Deval Patrick, da Tom Steyer da wasu tsiraru da ke fadi tashin ganin an andama da su, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen muhawarar zaben fidda gwani a nan gaba.