Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalli hotunan wurare masu muhimmanci a Iran
Bayan harin da Amurka ta kai wa Janar Qasem Soleimani wanda ya hallaka shi, Shugaba Donald Trump ya yi barazanar kai hare-hare wurare masu muhimmanci da tarihi a Iran matukar kasar ta mayar da martani kan harin.
Akwai daruruwan wuraren tarihi a kasar Iran. Hukumar raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta sanya sama da wurare 20 a kasar cikin kundinta.
Ga kadan daga cikin wuraren da muka zabo maku.
Daya daga cikin dandali mafi girma a duniya shi ne Naqsh-e Jahan (wanda yake da siffar tasawirar duniya a dunkule).
Wannan dandali yana birnin Isfahan, an gina shi a farkon karni na 17.
Sai kuma dandalin Naqsh-e Jahan da ke masallacin Imam (wanda aka sauya masa suna a shekarar 1979 bayan juyin-juya halin da kasar ta fuskanta).
An yi wa bango da kasan wurin ado mai ban sha'awa, sannan Unesco ta sanya shi cikin kundinta.
Fadar Golestan wuri ne da aka gina kamar ginin masarauta. An kawata ciki da waje da kaya masu ban sha'awa da daukar hankali a birnin Tehran.
Wannan fada ita ce ainahin wurin da masarautar Qajar ta zauna a karni na 19.
Persepolis ita ce babbar daular Achaemenid, da ta yi zamani a shekarar 515 BC.
A shekarar 1976 ne Unesco ta sanya ta cikin jerin wurare masu muhimmanci a duniya.
Daular Darius ta Achaemenid wadda ta yi zamani a shekarar 500 BC, wannan wuri wani katon dutse ne da aka yi wa rubutu da harsuna daban-daban.
Yana daga cikin rubutu na farko-farko da aka fara yi a zamanin.
Daya daga cikin gini mafi inganci da aka yi a duniya shi ne wurin tarihi na Arg-e Bam Citadel.
An yi amfani da kayan gini masu inganci wanda ke garin Silk mai dadadden tarihi a yamma maso gabashin Iran.
A shekarar 2003 wannan wuri ya kusan rushewa baki daya sakamakon mummunar girgizar kasar da ta afka a Iran.
Har yanzu ba a kammala sake gina wasu daga cikin wuraren ba.
Dogon ginin Azadi ko ginin 'yanci yana tsakiyar Iran ne.
Shugaban addini na kasar, Mohammad Reza Pahlavi, ne ya gina shi a lokacin bikin cika shekara 2500 da kafa kasar Iran.
An sauya wa ginin suna a shekarar 1976 lokacin juyin-juya halin da ya hambarar da mulkin Pahlani.
Wuri ne da ake yawan gudanar da tarukan addini na musulunci a kasar.
Wannan wuri ne da aka binne jagoran addini Ruhollah Khomeini, sannan akwai kabarin Ayatollah Ruhollah Khomeini da iyalansa- wanda shi ya kafa jamhuriyar musulunci a kasar.
Wannan wuri yana da matukar muhimmanci ga masu ziyarar addini a kasar Iran.