Yadda mata ke kallon uwar mijinsu a India

Asalin hoton, Getty Images
Ana cewa akwai matan aure masifaffu da kuma mazan aure da ke daka tsawa da turbune wa matansu fuska, sai dai duk cikinsu babu wanda ya kai isa da mallakar uwar miji.
Akasari ana yi wa uwar miji a Indiya kallon wata kasaitacciya mai ikon cewa a yi ko a bari, da ke fafutukar kwace iko a hannun surukarta wato matar danta, ga kuma nuna isa a kan dan nata da ma sauran mutanen gida.
Tauraruwa ce da ta yi fice a wani shirin wasan kwaikwayo a Indiya wanda akan fassara sunansa da: "Ai ita ma uwar mijin, ta taba zama matar dan wata.''
A yanzu, uwar miji a Indiya wata aba ce da masana ke gudanar da wani gagarumin bincike mai yiwuwa ma shi ne irinsa na farko a kanta.

Asalin hoton, AFP
Da yake mafi yawan mata a wannan yanki na Indiya kan tare a gidan dangin miji ne idan sun yi aure, alakar da suke kullawa da uwar miji tana da matukar muhimmanci.
Kuma fadi-tashinsu na rayuwa a wasu lokuta na ba da gudunmawa a kan gagarumin sunan da uwar miji ke yi.
A 2018, masu bincike daga Boston din Amurka da kuma birnin New Delhi sun zanta da matan aure 671, wadanda shekarunsu suka kama daga 16 zuwa 30 daga kauye 28 cikin lardin Jaunpur na jihar Uttar Pradesh, jihar masu ra'ayin mazan jiya da ke da yawan hada-hada da yawan mutanen da suka kai al'ummar kasar Brazil.
Mafi yawan matan dai Hindu ne kuma rukunin kasa na al'umma. Kusan kashi saba'in cikin 100 na matan na zaune ne a gida daya da uwar miji.
Masu binciken sun yi wa matan tambaya a kan huldarsu da danginsu da kawaye a wajen gidajensu. An tambaye su yawan ikon da uwar mijinsu ke da shi kan yadda suke kulla alaka da wasu.
Da Kuma tasirin hakan ga 'yancin cin gashin kansu da hanyar samun ayyukan lafiya da dabi'arsu ta neman magani.
Abin da masu binciken suka gano ga alama ya dusashe shingen da ke tsakanin almara da rayuwar zahiri.
Sun gano cewa matan da ke zaune tare da uwar miji na da takaitaccen 'yancin walwala da na kulla alaka da wasu a waje.

Asalin hoton, Getty Images
An dauka cewa yawan shigi da fice na iya taimaka musu wajen samun karin bayanai, da kulla zumunci da kawaye, da samun kwarin gwiwar yarda da kai da habaka burin rayuwa.
Haka zalika, shawarar da za su cimma dangane da lafiya da haihuwa ko tsarin iyali tana da alaka da irin wadannan kawanyen hulda.
Kimanin kashi 36 cikin 100 na matan da aka zanta da su ba su da kawa ko dangi na kut da kut a daukacin lardin, kashi 22 cikin 100 ba su da kawa ko dangi na kusa a ko'ina.
Kashi 14 ne kawai ake bari su fita zuwa asibiti su kadai, kashi 12 cikin 100 ne kawai ake bari su ziyarci kawaye ko danginsu a kauye ba tare da dan rakiya ba.

Asalin hoton, ROBERT NICKELSBERG/GETTY IMAGES
Haka kuma masu binciken sun gano kashi 18 cikin 100 ne na matan da ke zaune da uwar miji ke da aminai kalilan a kauyensu.
Uwar mijin takan takaita huldodinta na zamantakewa ta hanyar hana ta zuwa unguwa ita kadai ta yadda za ta sa ido kan halayyarta game da batun haihuwa da tsarin iyali.
A wasu lokutan uwar miji ta fi suruka muradin a haifa mata karin jikoki takamaimai ma ta fi son a haifa mata maza.
Kashi 48 cikin 100 na matan sun dauka cewa uwayen mazansu ba sa son ba da tazarar haihuwa. Binciken ya kuma gano cewa idan miji na tafiya zuwa ci-rani, uwar miji ta fi nuna isa kan zirga-zirga da huldodi da walwala da 'yancin cin gashin kai da yanke shawara.











