Sabuwar Shekara: Za a haifi 'yara 26,000' a Najeriya

Asalin hoton, @UNICEF_Nigeria
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya ce an yi kiyasin cewa yara 26,039 ne za a haifa a Najeriya a ranar sabuwar shekara.
Jariran da za a haifa a Najeriya za su zama kashi 7 ciikin 100 na jarirai 392,078 da za a haifa a fadin duniya a ranar sabuwar shekarar.
Najeriya dai ita ce ta uku a haihuwar da za a yi bayan Indiya da China.
Ga jerin kiyasin yawan yaran da za a haifa:
- Indiya — 67,385
- China — 46,299
- Najeria — 26,039
- Pakistan — 16,787
- Indonesia — 13,020
- Amurka — 10,452
- Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo — 10,247
- Ethiopia — 8,493
A kowace shekara, hukumar UNICEF na murnar sababbin yaran da aka haifa a ranar sabuwar shekara.
A shekarar 2018, yara miliyan 2.5 ne suka mutu a farkon watan da aka haife su a fadin duniya; kusan kashi ukun su a ranar da aka haife su ne suka mutu.
A Najeriya kusan yara 318,522 ne suka mutu a irin haka, ma'ana a farkon watan da aka haife su a shekarar 2018.
Cikin yaran, akasarinsu sun mutu ne sakamakon cututtukan da za a iya daukar mataki kansu da kuma matsalolin da suke bijirowa yayin haihuwa.
Bugu da kari, sama da yara miliyan 2.5 ne ake haihuwarsu a mace a duk shekara, inda dubu 400 daga Najeriya suke.











