An zargi MTN da ba Al Qa'ida da Taliban cin hanci

Afghanistan

Asalin hoton, AFP Contributor

Bayanan hoto, Jami'an Amurka 2,400 suka mutu a Afghanistan tun kaddamar da farmaki a 2001

Kamfanin sadarwa mafi girma a Afirka MTN ya ce yana nazari kan zargin cewa ya biya wasu kudade na kariya ga mayaka masu da'awar jihadi a Afghanistan.

Zargin wanda aka gabatar a wata kotun Amurka a ranar Juma'a, ya ce kamfanin ya saba dokokin yaki da ta'addanci na Amurka.

An shigar da karar ne a madadin iyalan Amurkawa da aka kashe a hare hare a Afghanistan.

Akwai kuma wasu kamfanoni da cikin bayanan da aka gabatar a kotu da ake zargi.

An zargi MTN ne da biyan cin hanci ga al Qa'ida da Taliban domin kaucewa saka jari ga yanayin tsaro mafi tsada domin sadarwa.

Kudaden da ake zargin MTN ya biya ya taimakawa Taliban wajen kai hare-hare a Afghanistan tsakanin 2009 da 20017, kamar yadda aka shigar a kotun.

An yi zargin cewa kudaden sun taimaka wajen biyan wasu bukatun 'yan ta'addan, "wanda kuma ya saba dokar yaki da ta'addanci."

Amma kamfanin ya musanta zargin, inda ya ce yana gudanar da kasuwancinsa ta hanyar bin doka a dukkanin yankunan da yake.

MTN shi ne kamfanin sadarwa mafi girma a Afirka, kuma na na takwas a duniya, inda yake da masu amfani da shi sama da miliyan 240.

A shekarar 2015 an taba cin tarar kamfanin na kasar Afirka ta kudu MTN a Najeriya dala biliyan biyar don kin bin umarnin gwamnati na katse layukan mutum miliyan biyar da ba a yi musu rijista ba.