Hotunan duniyar wata da suka fi burgewa a 2019

    • Marubuci, Daga Paul Rincon
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science editor, BBC News website

Yayin da 'yan sama-jannati suka yi manyan tafiye-tafiye zuwa duniyar wata, sun dauko hotunan duniya daga duniyar rana a shekarar 2019. Ga wasu daga cikinsu.

Daga gira-gizai

hoton Jupiter da aka dauko daga jirgin NASA mai suna Juno

Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech/SwRI/MSSS/Kevin M. Gill

Tun bayan saukar jirgin hukumar kula duniyar wata ta Amurka NASA mai suna Juno a duniyar Jupiter a shekarar 2016, ya yi ta aiko kayatattun hotunan gira-gizai. An hada wannan hoton ne daga wasu surorin da aka dauko hotunansu daga jirgin a ranar 29 ga watan Mayu.

An dauki hoton ne a lokacin da Juno ke tafiya kusa da Jupiter daga duniyar rana a tazarar kilomita 18,600 da kilomita 8,600 daga saman giragizai.

Jupiter from Juno

Asalin hoton, Kevin McGill/NASA/JPL-Caltech/SwRI/MSSS

Hoton da ke sama na nuna gira-gizai a zagaye da wani mulmulallen abu a duniyar Jupiter.

Mutummutumi

Arrokoth

Asalin hoton, NASA/JHUAPL/SWRI/T. Appere

Bayanan hoto, Hoton Arrokoth

Bayan isar Juno duniyar Pluto a 2015, sai aka tura shi zuwa Kuiper da ke gaba da duniyar Neptune. Kuipter na cike da wasu abubuwa masu kankara da ke nuna yadda duniyar rana ta fara.

Masana kimiyya sun yi ittifaki a kan wata halitta mai suna MU 69 wanda aka gano a shekarar 2014. MU 69 wanda yanzu ake kira Arrokoth na da tsawon kilomita 39. Ya kunshi wasu kwallayen kankara guda biyu da ke yin karo da juna idan suna tafiya a hankali. Launin ja ja da suke yi na faruwa ne saboda sunadarin tholins da ke jikinsa.

Tartsatsin wutan Stellar

Eta Carinae

Asalin hoton, NASA/Esa/N. Smith/J. Morse

Bayanan hoto, Eta Carinae

Eta Carinae rukunin taurari ne masu nisan shekara 7,500 na haske tsakani. Eta Carinae ya kunshi taurari akalla guda biyu, da idan aka hada su suke samar da makamashin da ya ninka wanda rana ke samarwa sau miliyan biyar. Daya daga cikin taurarin na fitar da iskar gas da ke sandarewa ya koma wasu tantani guda biyu. Masana duniyar taurari sun dade suna tunanin ko tantanin zai rubewa har ya tarwatse.

Martian selfie

Mars Curiosity rover

Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech/MSSS

Bayanan hoto, Jirgin Mars Curiousity na Nasa

Tun shekarar 2012 jirgin sama jannatin Nasa a duniyar Mars mai suna Mars Curiousity Rover ke bincike a Gale Crater a duniyar Mars. Butunbutumin ne ya dauki kansa wannan hoton Selfie a sadda ya isa kwarin tsaunin Sharp - wanda shi ne wuri mafi zurfi.

Samfurin duwatsu biyu da aka hako daga wurin sun nuna akwai laka mai yawa. Laka na samuwa ne a wurin da ke da ruwa wanda babban jigo ne ga rayuwa. Hujjojin da aka samu a baya sun nuna cewa ruwa ya taba taruwa a Gale Crater.

Duniyar wata

Jirgin duniyar wata

Asalin hoton, CLEP

Bayanan hoto, Jirgin duniyar wata

A ranar 3 ga watan Janairun wannan shekara ne jirgin tawagar Chang'e-4 na kasar China ta zama wanda ya fara sauka da doron duniyar wata. Kwanaki kadan bayan saukar jirgin ne aka umurci kyamarorin da ke jikinsa su dauki hoton juna.

Chang'e-4 lander

Asalin hoton, CLEP

Jiragen sama-jannatin na dauke da kyamarori da nau'arar auna yanayin doron duniyar wata da na'urar gano irin ma'adanai da kuma wurin gwajin kai tsaye na yiwuwar shuka a duniyar wata.

A watan Mayu masana kimiyya na kasar China sun fitar da rahoto cewa Chang'e-4 ya tabbatar da samuwar wani kwari a doron duniyar wata a ina jirgin ya sauka.

A galactic rival

NGC 772

Asalin hoton, ESA/Hubble & NASA, A. Seth et al.

Bayanan hoto, NGC 772

Hoton nan da aka dauka da na'uar hangen nesa ta Hubble ya nuna tarin taurarin da ake kira NGC 772 masu tazarar shekara miliyan 130 na haske. Yawancin siffofin NGC 772 suna kama da duniyar taurarin da muke ciki wato Milky Way Galaxy. Misali shi ne, Milky Way da NGC 772 kowannensu na da wasu kananan taurari masu tafiya kusa da manyan taurari.

Sai dai kuma sun bambanta ta wasu muhimman fuskoki. Misali shi ne, NGC 772 ba shi da abin da ake kira Bar, wanda aka yi daga gas da taurari. Ana hasashe cewa Bar ne ke saita abubuwa masu zuwa duniyar taurari - ko haddada samuwar taurari.

Muna tashi

Lightsail 2

Asalin hoton, Planetary Society

LightSail wani shiri ne da wata kungiya mai zaman kanta wato The Planetary Society ta kafa. Manufar ita ce nuna yadda saukar lema ke tafiya a ban kasa. Masana sun jima suna tattaunawa a kan lemar wato Solar sail a matsayin abin da zai taimaka wajen harba jirgi zuwa duniyar wata.

An kaddamar da LightSail 2 ne a ranar 25 ga watan Yunin 2019. Wannan hoton ya nuna yadda lemar bayan dan fara amfani da shi a ranr 23 ga watan Yuli.