Najeriya: An kona coci kan batan wani yaro a Akure

Wasu masu zanga-zanga sun kona wani coci a birnin Akure da ke kudu maso yammacin Najeriya, sakamakon jita-jitar cewa an gano gawar wata yaro dan shekara daya da ya bata, a cikin mumbarin cocin.
Ganau sun ce 'yan sanda sun harbi masu zanga-zangar biyu a yayin da jami'an tsaron ke kokarin tarwatsa taron.
'Yan sanda sun ce an kashe jami'insu daya.
A watan da ya gabata ne yaron mai suna Sotitobire Miracle ya bata, a yayin da ya je cocin tare da mahaifiyarsa.
Ba a san takamaimai yadda yaron ya bace ba, amma mahaifiyarsa Modupe Kolawole, ta shaida wa BBC cewa tana zargin wasu mugaye da aikata hakan.
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta kama Alfa Babatunde, wanda shi ne mamallakin cocin a makon da ya gabata, kan batan yaron.
Har yanzu dai bai ce komai ba kan batun.
Wakiliyar BBC ta sashen Yarbanci Temitope Adedeji wacce ta halarci cocin ta ruwaito cewa babu tabbas ko an gano gawar yaron.











