Sarkin Bichi ya sauke Hakiman Kano saboda kan kin yi masa mubayi'a

Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauke wasu hakimai saboda kin yi masa mubayi'a.
Hakimai biyar ne sarkin ya sauke inda tuni ya maye gurbinsu da wasu.
Hakiman da aka cire sun hada da Bichi da Dawakin Tofa da Dambatta da Minjibir da kuma na Tsanyawa.
Wannan na zuwa ne bayan da majalisar jihar Kano ta sake yin wata doka wadda ta kafa sabbin masarautu guda hudu wadanda kotu ta soke a watan da ya gabata.
Kotun ta sanya ranar Talata domin fara sauraron karar.
Kwanaki kadan bayan kafa dokar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya nada Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar inda ya umurce shi da ya kira taron zauren.
Har yanzu dai Sarkin bai kira taron ba inda masarautar Kano ta sake maka gwamnatin jihar Kotu kan kafa sabbin masarautu a jihar.
- Madakin Kano Hakimin Dawakin Tofa Alhaji Yusuf Nabahani, wanda shi ne shugaban masu zaben Sarkin Kano.
- Sarkin Bai Hakimin Dambatta Alhaji Mukhtar Adnan, daya daga masu zaben Sarkin Kano. Ya zama Hakimin tun 1954, abin da ya sa ya fi kowane Hakimi dadewa a masarsutar Kano, domin kuwa ya shafe shekara 64 yana Hakimci kafin a sauke shi a ranar Asabar din nan.
- Matawallen Kano Hakimin Minjibir Aliyu Ibrahim Ahmed.
- Barden Kano Hakimin Bichi Alhaji Idris Bayero, wanda uba yake ga Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero.
- Hakimin Tsanyawa Alhaji Sarki Aminu.
Biyu daga cikin Hakiman da aka cire wato Madaki da Sarkin Bai na cikin mutum hudu da suka shigar da karar gwamnan Kano kan sababbin sarakunan da aka nada gaban kotu.
Suna kalubalantar kirkirar sababbin masarautu sannan suka nemi kotu ta hana wadanda aka yi kara sauke su daga mukamansu ko daukar wani mataki da zai taba aikinsu na masu zaben Sarki.
Masarautar Kano na daga cikin wadanda suke da tarihi da shekaru da dama a kasar Hausa.
An yi sarakunan Habe sama da 40 kafin Fulani suka karbi mulki a shekarar 1806 inda Sarki mai ci a yanzu Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne na 14 a jerin Fulani ke mulki bayan da ya gaji Ado Bayero, a 2014 wanda kuma shi ne mahaifin Sarki Bichi na yanzu, Aminu Ado Bayero.

Asalin hoton, SALISHU TANKO YAKASAI/FACEBOOK











