Masarautun Kano: Martanin gwamnati ga umurnin kotu

Gwamna Ganduje da Aminu Ado Bayero

Asalin hoton, Salihu Tanko Yakasai

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani ga umurnin babbar kotun jihar da ta dakatar da gwamnatin daga kafa sabbin masarautu a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Garba Muhammad ya fitar, ya ce umarnin kotun bai shafi samuwar sabbin masarautun da gwamnatin jihar ta kafa ba.

Sai dai kuma Antoni Janar kuma kwamishinan shari'ar jihar ya ba wa BBC tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta bi umurnin kotun game da matsayin masu nada sarki.

Kotun ta bayar da umurnin ne kwana biyu bayan gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya nada sarkin Kano Muhammadu Sanusi a matsayin shugaban majalisar sarakunan.

Masu nada sarki a Masarautar Kano ne suka shigar da karar suna neman kotun ta dakatar da gwamnatin da majalisar dokokin jihar kafa sabbin masarautun Bichi da Gaya da Karaye da kuma Rano da kuma kafa majalisar sarakunan jihar.

Kotu za ta cigaba da sauraron karar a ranar 17 ga watan Disamban nan da muke ciki.