Dahiru Bauchi ya yi magana kan raba masarautar Kano

Bayanan bidiyo, Dahiru Bauchi game da raba masarautar Kano

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wa BBC karin bayani dangane da ra'ayinsa a kan rarraba masarautar Kano.

Ya bayyana cewa ko Turawan mulkin mallaka ba su rarraba masarautun Kano ba, kamar yadda gwamnatin Kano ta yi a wannan lokaci.

Ya kuma yi karin bayani game da harkokin tsaro da halin da mutane suka tsinci kansu a Najeriya.