Mane tamkar yaya yake a wurina, ya taimaka mani sosai - Sarr

Asalin hoton, Getty Images
Dan asalin kasar Senegal kuma dan wasan Watford Ismaila Sarr, ya bayyana yadda shahararren dan wasan Senegal kuma fitacce a Livepool Sadio Mane, ya taimake shi a Ingila.
Sarr wanda Watford ta saya a kan kudi fam miliyan 25 daga Rennes ya shaida wa BBC yadda Mane ya taimaka masa lokacin da ya koma Ingila.
Mai shekara 21 din ya ce "Sadio yana bani shawara a ko da yaushe. Muna yawan magana da shi, tamkar babban yaya yake a wurina" in ji Sarr.
"Lokacin da na iso, ya aiko mani da sako 'barka da zuwa firimiyar Ingila', 'sannu da zuwa Ingila,' muna kuma magana a kungiyarmu ta gida.''
"Ya ba ni shawarwari, na kuma yi kokarin dabbaka su. 'Idan ba ka wasa, ka natsu, ka ci gaba da yin aikinka', komai zai daidaita'. Abin da ya ce mani ke nan. Sai ni kuma na yi hakan."
Kamar dai Mane, Sarr ya fara taka leda ne a makarantar horon wasan kwallon kafa ta Generation Foot da ke a babban birnin Senegal Dakar, kafin ya tafi zuwa Metz da ke a Faransa.

Asalin hoton, EPA
"Bayan an mayar da ni Rennes daga Metz, ina kallon bidiyoyin wasan Sadio, yadda ake gudu da yadda yake yanka a wasansa, ina kallon komai nasa, a cewar Sarr.
Sarr ya buga wa Senegal wasa 26 izuwa yanzu, inda ya zura kwallo hudu. Ya buga wasa tare da Mane a gasar cin kofin zakarun Afirka da aka yi a Masar inda Algeria ta fitar da su bayan da aka tashi daya da nema a wasan karshe na lashe gasar.











