Masu zanga-zanga sun tarwatsa zaben shugaban kasan Algeria

Asalin hoton, EPA
Masu zanga-zanga kin amincewa da zaben shugaban kasa a Algeria sun tarwatsa rumfunan zabe a yankin Kabylie da ke gabas da Algiers babban birnin kasar.
Ana gudanar da zaben ne bayan tilasta wa tsohon shugaba Abdelaziz Bouteflika, yin murabus bayan shekara 20 yana jagorancin kasar.
Bouteflika ya sauka ne a watan Afrilu bayan zanga-zangar kyamar gwamnatinsa da aka shafe makonni a na yi a kasar.
Masu zanga-zangar sun cigaba da bukatar kakkabe ragowar jami'ai da mukarraban gwamnatin Abdelaziz Bouteflika, daga shugabancin kasar.
Suna kuma barazanar kaurace wa zaben na yau Alhamis. Akalla rumfunan zaben guda biyu ne cincirindon masu zanga-zangar suka mamaye a yankin inda suka tarwatsa al'amura.
Dukkan 'yan takara biyar a shugaban kasar na yau Alhamis mukarraban tsohon shugaban ne.
Masu lura da al'amura na ganin rundunar sojin Algeria na tunanin cewa zaben ita ce kadai hanyar da za ta daidaita al'amura a kasar.







