Me ya sa ba a jin kan 'yan Burtaniya?

Crowd Shouting

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Lucy Rodgers
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Tun da aka yi zaben raba gardamar ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai ake ta ce-ce-ku-ce kan rabuwar kasar ta fannin kudi da ilimi da shekaru.

Sai dai duk da rarrabuwar kawuna tsakanin masu so kasar ta kasance a EU da masu so ta fice, mafi yawan mutane a Burtaniya ba su da rarrabuwar kawuna kan abubuwa da yawa, kuma mutane ne masu saurin karbar sauyi.

Ga abubuwa 10 da suka hada kan mafi yawan 'yan Burtaniya, kamar yadda sakamakon wani binciken jin ra'ayin mutane ya nuna.

1. Tsare kawunanmu ga iyalanmu

Couple holding hands

Asalin hoton, Getty Images

Kusan duk 'yan Burtaniya - kashi 99 cikin 100 - na ganin ya dace su kame kansu ga iyalansu kawai, a cewar wani bincike da COMRES ya gudanar wa BBC.

Mata sun fi ganin dacewar haka fiye da maza - cikin wadanda aka yi binciken a kansu, kashi 86 cikin 100 na mata na ganin dacewar tsare kai ga iyalai, sabanin kashi 79 cikin 100 na maza.

Presentational white space
Short presentational grey line

2. Amincewa da daidaito wajen biyan albashi

Men and women at work

Asalin hoton, Getty Images

Kusan kowa ya amince da a samu daidaito wajen biyan albashi tsakanin maza da mata, a cewar wani bincike da British Social Attitudes ya gudanar.

Cikin wadanda aka yi binciken a kansu, kusan mutum tara cikin 10 (wato kashi 89 cikin 100) sun ce ba daidai ba ne a biya maza fiye da matan da ke aiki iri daya a ma'aikata daya.

Presentational white space
Short presentational grey line

3. An daina ganin cewa aikin mace shi ne ta kula da gida.

Coder

Asalin hoton, Getty Images

"Kashi uku cikin hudu na 'yan Burtaniya sun yi watsi da tunanin cewa mace ta zauna ta kula da gida yayin da maza kuma za su fita su yi aiki", a cewar bayanai daga BSA.

Haka kuma, mafiya yawan 'yan kasar na ganin cewa maza da mata za su iya yin aiki iri daya ciki har da zama likita ko kansila ko 'yar majalisa, a cewar binciken.

Presentational white space
Short presentational grey line

4. Ganin cewa 'babu laifi a yin luwadi da madugo'.

Couple with noses touching

Asalin hoton, Getty Images

Mutum biyu cikin uku na 'yan Burtaniya sun ce luwadi da mudugo ba laifi ba ne, a cewar binciken BSA. An samu karuwar kusan kashi 50 cikin 100 daga lokacin da aka fara yin tambayar a 1983.

A cewar binciken, karuwar alkaluman bai kebanta da sauyin da aka samu a matasa ba, tsofaffi da kuma marasa addini su ma sun sauya tunaninsu kan wannan batu.

Short presentational grey line

5. Goyon bayan 'yancin mace ta zubar da ciki.

Two sets of hands

Asalin hoton, Getty Images

Kusan kashi 92 cikin dari na 'yan Burtaniya na goyon bayan zubar da ciki idan rayuwar mace na cikin hadari, a cewar binciken BSA.

Tun shekarar 2005, goyon bayan zubar da ciki idan mace ba ta ra'ayin daukar cikin ya karu daga kashi 60 zuwa kashi 69 cikin dari.

Short presentational grey line

6. Amincewa da ilimin kimiyya da masu ilimin kimiyyar.

Scientists

Binciken BSA ya nuna cewa sama da 'yan Burtaniya 8 cikin 10 sun amince da masana kimiyya kuma kashi 67 cikin dari sun amince da kamfanonin kimiyya.

Kashi 94 cikin 100 sun yarda cewa bincike kan kiwon lafiya zai haifar da rayuwa mai inganci nan gaba.

Presentational white space
Short presentational grey line

7. Sun amince da hukumar NHS.

Nurse

Asalin hoton, Getty Images

Kusan kashi 77 cikin 100 na 'yan Burtaniya sun yarda cewa Inshorar Lafiya ta NHS na da matukar muhimmanci ga al'ummar kasar, a cewar wani bincike da Ipsos Mori ya yi wa King's Fund.

Wannan goyon bayan ya kasance haka tsakanin gwamnatoci da dama.

Short presentational grey line

8. Yarda da cewa gidan sarautar kasar na da muhimmanci.

Royal parade in London

Asalin hoton, Getty Images

Sama da 'yan Burtaniya 7 cikin 10 sun yarda cewa gidan sarautar Ingila na da matukar muhimmanci ga kasar, kamar yadda binciken BSA ya nuna.

Sai dai, yawan mutanen da suka yarda da haka ya ragu sosai tsakanin shekarun 1980 da 1990, kafin ya sake karuwa a shekarun 2000.

Amma wasu abubuwa da suka faru a gidan a 'yan shekarun nan sun kara wa wannan ra'ayi karfi: Auren William jikan Sarauniya da matarsa Kate a 2011 da kuma auren kanensa Harry da matarsa Meghan a 2018 da haihuwar jikokin sarauniyar.

Short presentational grey line

9. Tunanin cewa mutane ne ke janyo sauyin yanayi.

Smoke from industry chimneys

Asalin hoton, Getty Images

Kashi 95 cikin 100 na 'yan Burtaniya na tunanin cewa mutane na taka rawa wajen jawo sauyin yanayi, kamar yadda wani binciken European Social Survey ya nuna.

Wasu kashi 36 cikin 100 sun ce sauyin yanayi na faruwa ne sakamakon ayyukan bil Adama, yayin da kashi 53 cikin 100 suke ganin ayyukan mutane da abubuwan da ke faruwa daga Allah ne ke haifar da sauyin yanayi.

Presentational white space
Short presentational grey line

10. Son David Attenborough, kungiyoyin agaji na lafiya, kamfanonin Heinz da Lego da Google Maps da Malteasers

David Attenborough

Asalin hoton, Getty Images

Idan aka zo batun abubuwa - sanannun mutane da kungiyoyin agaji da abinci, sune suka mamaye jerin abubuwan da 'yan Burtaniya suka fi so a cewar kamfanin bincike na YouGov,

David Attenborough, mai gabatar da shirye-shirye a Talabijin shi ne na farko a jerin abubuwan da 'yan Burtaniya ke so.

Daga shi kuma sai kungiyoyin agaji na St John Ambulance Brigade da Macmillan Cancer Support da tauraron fina-finan Amurka, Tom Hanks.

Presentational white space
Short presentational grey line