Wasikar 'yan Najeriya zuwa ga Shugaba Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Fiye da wata shida ke nan tun bayan da aka rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a wa'adin mulki karo na biyu.
Wannan ya sa muka tambayi masu bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta da idan suka samu damar rubuta wa Shugaba Buhari wasika, me za su ce masa?
A shafinmu na Facebook mutum sama da dubu 360 sun gan sakon, an yi tsokaci fiye da 7,000, an so shi fiye da sau 7,000 cikin kasa da sa'a 24.
Yayin da wasu suka soki salon mulkin shugaban, akwai wadanda suka ba shi shawara, har ila yau, akwai kuma masu yaba masa.
Daga shafinmu na Facebook, Kabiru Suleiman shawara ya bai wa Shugaba Buhari, inda ya ce:
"Idan na samu damar rubuta wa Shugaba Buhari wasika zan ce masa a matsayinsa na dattijo, ya gyara salon mulkinsa ya rinka duba wadanda ya nada wakilansa da ayyukun da suke gudanarwa musamman akan tsaron kasa mu."
"Zan kara tunatar da shi akan alkawuran da ya yi wa talakawa na cewa da su yi hakuri za su ga sa har da kahonsa."
"Baya ga haka, an yaudari al'umma game da wutar lantarkin kasar nan wanda har yanzu ba mu ga komai ba, ci gaban wutar lantarki sai kara komawa baya yake."
"Daga karshe idan ya yi alkawari ya cika domin kare mutuncinsa domin da yawa wasu na ganin ya zama dan siyasa kuma makaryaci saboda dukiyar kasa da ake cewa an karba a hannun barayin gwamnati talaka bai san me aka yi da kudaden, ko me za a yi da su ba, shiru kake ji," in ji shi.
Shi kuwa Abubakar Umar Faruk hada shi da Allah ya yi: "Yaji tsoron Allah, anajin jiki a mulkinsa," in ji shi.
Abdullahi Adamu addu'a ya yi masa: "Fatan nasara da gama lafiya gami da addu'a Allah ya taimake shi bisa amanar da ke kansa."
A Twitter kuma an samu sakonni kamar:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Karshen labarin da aka sa a X, 4
A shafin Instagram kuwa an so shi sau kusan 4000 kuma an yi tsokaci fiye da sau 600:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram
Sharhi
Wannan jin ra'ayi dai ya nuna cewa 'yan kasar na fatan su samu damar da za u gana da Shugaba Buhari ko da takaitacciya ce don amayar da abin da ke cikinsu game da salon mulkinsa.
Da dama na son su isar da fatan alkhairin da suke masa ne, yayin da wasu kuwa korafi ne fal a cikinsu da suke son isar wa.
Abubuwa da dama ne suka sa 'yan Najeriyar ke begen Buhari ya yi duba a kansu, kamar sha'anin taro da tattalin arziki da shawo kan hauhawar farashi da samar da ayyukan yi da sauransu.