Babu ranar bude iyakokin Najeriya – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu bai sa ranar bude iyakokin kasar da aka rufe ba, har sai an shawo kan matsalar shigo da kayan da aka haramta a kasar.

Shugaban Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya gana da wata tawagar Dattijan Jihar Katsina a mahaifarsa ta Daura, kamar yadda mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Ya kuma ce yawan man fetur da ake amfani da shi a kasar ya ragu da kusan kashi 30 cikin 100 bayan da aka rufe iyakokin kasar.

Malam Garba Shehu ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta yi amfani da irin matakan da ta dauka wajen rufe iyakoki don farfado da bangaren noma.

Ya ce hakan zai sa kasar ta adana biliyoyin nairori da a baya take kashewa wajen biyan kudin shigo da kaya.

Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari ya jinjina wa Shugaba Muhammadou Youssoufou na Jamhuriyar Nijar kan korar wasu jami'ai da kuma haramta ajiye kayan da ake shirin yin fasa kwabrinsu zuwa Najeriya.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari ya tausaya wa mazauna garuruwan da ke kan iyakoki bisa haramta sayar da man fetur a garuruwansu, kuma ya ce gwamnatinsa ta dauki wannan matakin ne don "kare martabar manoma".

Ya ruwaito shugaban da cewa "rashin gaskiya ya zama ruwan dare a kasarmu."

Haramcin siyar da man fetur a wadannan garuruwa dai ya janyo rufe duka gidajen mai a yankunan kuma wannan haramcin ya shafi har da Daura, mahaifar Shugaba Buhari.

Buhari ya ce haramtawar na dan wani lokaci ne kafin Hukumar Custom ta tantance ainihin masu sayar da mai da kuma gidajen man da ake amfani da su wajen fasa kwabrin haramtattun kaya.