Ana zargin Johnson da 'zagin' 'yan Najeriya

A

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar 1999 ne Mista Johnson ya rubuta makalar

Saura mako biyu 'yan Birtaniya su fita don kada kuri'a a zaben gama gari, wata jarida ta wallafa tsohuwar makalar da Firai Minista Boris Johnson ya rubuta a ciki ya zagi 'yan Najeriya.

Mista Johnson dai tsohon dan jarida ne kuma ya rubuta makalar a shekarar 1999, kan yadda za a iya janyo hankalin matasa su shiga jam'iyyar Conservative.

Wani mai yaki da wariyar launin fata Weyman Bennett ya shaida wa jaridar Guardian ta Birtaniya cewa kalaman Mista Johnson ''tsantsar wariyar launin fata ne.''

BBC ta tuntubi jam'iyyar Conservative kan batun.

A shekarar 2002 Mista Johnson ya nemi afuwa kan wani rubutu da ya yi inda ya ke sukar tafiye-tafiyen Mista Blair kasashen waje.

"An ce sarauniya na kaunar kasashen Commonwealth, watakila saboda yadda suke daga tutar kasar nan a kasashensu...

"An ce zai yi balaguro zuwa kasar Congo. Babu tantama idan ya je ba za a ji karar harbin bindigar AK47 ba, masu fada da juna su ma za su tsahirta, sannan kabilun da ba sa ga-maciji da juna za su yi ta dariyar yake...;;

Kalaman Mista Johnson kan 'yan Najeriya sun tayar da kura da janyo cece-kuce, a dai-dai lokacin da ake yaki da kalaman kiyayya da wariyar launin fata a jam'iyyar adawa ta Labour.