Trump ya kai wa dakarun Amurka ziyarar ba-zata a Afghanistan

US President Donald Trump sits down for Thanksgiving dinner with US troops at Bagram Air Field

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Trump ya ci abincin Cika Ciki tare da sojojin Amurka

Shugaba Donald Trump ya kai wa dakarun Amurka da ke Afghanistan wata ziyarar ba-zata - a karo na farko da ya taba zuwa kasar - a hutun Bikin Cika Ciki, wato Thanksgiving.

A yayin da ya je filin daga na Bagram Airfield, Mista Trump ya yi ta zuba wa sojojin abinci kamar naman talo-talo, ya kuma dauki hotuba da su sannan ya gana da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani.

A wani jawabi da ya gabatar wa dakarun, Mista Trump ya ce Amurka na tattauna wa da Taliban, inda ya ce "suna son a kulla yarjejeniya."

Mista Trump ya kuma ce "a hankali" Amurka na rage yawan dakarunta.

Akwai dakarun Amurka 13,000 a Afghanistan, shekara 18 bayan da Amurka ta shiga tsakani don murkushe Taliban, tun bayan harin 11 ga watan Satumbar 2001 da aka kai Amurkar.

Ziyarar na zuwa ne bayan da aka yi musayar fursunoni da Taliban, a wani fata na koma wa kan teburin sulhu.

A farkon watan nan ne, Taliban suka saki wasu malaman jami'a biyu na kasashen yamma, wadanda suke tsare tun shekarar 2016 - da Ba'amurke Kevin King da kuma dan Australiya Timothy Weeks - a matsayin musayarsu da manyan mayakanta uku da ke tsare.

Da yake magana a sansanin da ke kusa da babban birnin kasar Kabul, Shugaba Trump ya ce: "Za mu gana da 'yan taliban kuma mun ce dole ne a tsagaita wuta, amma sun ce ba sa son hakan, yanzu kuma sun ce suna so a tsagaita wutar.

"Na yi amanna hakan zai fi."

Ba a yi bayani sosai kan yadda muhimmancin tattaunarwa ya kasance ba.

Tun da dadewa jami'an Afghanistan suka so a tsagaita wuta amma Taliban, wadanda a yanzu suke iko da yankuna masu yawa da a baya ba su da shi tun bayan hambarar da su a 2001, suka ki yin tattauna wa kai tsaye da gwamnatin, har sai da aka amince kan yarjejeniyar Amurka.

Shugabannin Taliban sun tabbatar da cewa sun gana da manyan jami'an Amurka a Doha tun karshen makon da ya gabata, amma dai har yanzu ba a fara tattaunawa bisa tsari ba, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Mista Trump ya kuma tabbatar da shirinsa na rage yawan dakaru zuwa 8,600, amma bai fadi yawan dakarun da za su tafi ba da kuma lokacin.

"Za mu ci gaba da kasancewa har sai mun kulla yarjejeniya ko kuma mun samu nasara, kuma suna so su kulla yarjejeniya marar kyau."

Me kuma ya faru yayin ziyarar?

Mista Trump ya isa kasar a ranar Alhamis da misalin karfe 8:30 na daren can, sannan kuma ya tafi a cikin daren, a wata tafiya mai tsananin sirri saboda tsaro.

Fadar White House ta tabbatar da cewa akwai wani shiri da aka yi na wallafa sakonni a shafin Twitter na shugaban a yayin tafiyar, domin dauke hankulan mutane daga zarge-zarge idan ba a ji duriyarsa ba tsawon lokaci.

Donald Trump with army personnel standing behind him in Afghanistan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Donald Trump ya ce Taliban "na son kulla yarjejeniya"

A yayin da ya isa, shugaban rundunar hadaka na sojojin Janar Mark Milley ne ya tarbi Mista Trump, wanda a ranar Laraba ya ce yiwuwar samun nasara a tatattaunawar zaman lafiya da ake yi ta fi ta baya armashi, kuma za a iya yi nan kusa."

Shugaban kasar, wanda ya tafi da mataimaka da dama, ya zuzzuba wa sojojin naman talo-talo, sannan ya zauna ya ci abincin Cika Cikin da su tare da daukar hotuna.

Trump ya ce "Babu inda zan zauna na yi Bikin Ranar Cika Cikin nan irin nan wajen, tare da jajirtattu, gwaraza kuma sojojin da suka fi kowa a duniya."

Shugaba Ghani na Afghanistan ya gode wa sojojin Amurka da suka dinga sayar da ransu a Afghanistan, yana mai cewa: "A yanzu dakarun tsaron Afghanistan ne za su jagoranci tafiyar."

Bayan ganawar tasu, Shugaba Ghani ya wallafa sako a Twitter amma bai ambaci kalaman Trump na yarjejeniya da Taliban ba, sai ya ce: "Dukkan bangarorin biyu sun jaddada cewa idan har Taliban da gaske take kan yarjejeniyar zaman lafiya, to sai sun amince da tsagaita wuta."

Sai dai Taliban ba ta mayar da martani kan lamarin ba, kuma mutane da dama na tambayar ko da gaske kungiyar za ta shiga cikin sasantawar tsakani da Allah.

Presentational grey line