'Amfani da magungunan gargajiya na munana cutar sankara'

Yana da muhimmanci masu fama da cutar kansa su shaida wa likitansu idan suna shan wani nau'in maganin gargajiya kan cutar, saboda a wasu lokutan abubuwan da aka yi amfani da su wajen hada maganin ka iya hana maganin asibiti yin aiki.

Magungunan da aka hada su da citta da tafarnuwa na janyo maganin asibiti samun tsaikon aiki ga maras lafiya, musamman mata da ke fama da cutar kansar mama idan ta fara yaduwa.

Likitan fida Farfesa Maria Joao Cardoso, ya ce babu wata sahihiyar shaidar da ke nuna magungunan gargajiya ko man shafawa na magance cutar, don haka idan ana tababa akan magani rashin amfani da shi ne ya dace.

Ita ma shugabar likitocin fidar kansar nono, a cibiyar da ke birnin Lisbon a kasar Portugal Farfesa Cardoso ta ce, "ya zama wajibi likitoci su zage damtse da matsawa marasa lafiya sanin irin magungunan da suke amfani da su idan ana musu maganin cutar kansa."

Ta ce abu ne mai matukar muhimmanci su ma marasa lafiya su dinga tuntubar likitocinsu kafin su yi amfani da kowanne maganin cutar kansa na gargajiya idan suna kan shan maganin asibiti.

Hadarin a nan shi ne yawancin magungunan gargajiya kan shafi tasirin maganin da ake bai wa maras lafiya a asibiti, wasu kuma kan daskarar da jini, wasu kan janyo magani ya dauki lokaci bai yi tasiri ba, hakan kuma babbar barazana ce.

Ta bayyana wasu daga cikin abubuwan da ake amfani da su a magungunan gargajiyar da ke mayar da hannun agogo baya a magance cutar kansa;

  • Citta
  • Ganyen da ake hada maganin zazzabi
  • Tafarnuwa
  • Ganyen ginkgo
  • Cittar yankin Asiya
  • Ganyen rai dore
  • Gyadar Turawa
  • Turmeric wato kurkur

'Za su iya cutarwa'

Farfesa Cardoso ta ce ba abin mamaki ba ne don marasa lafiya sun nemi wani maganin na daban baya ga wanda ake ba su a asibiti, su na hakan ne da tunanin dacewa. Sai dai ta ce ya kamata mutane su san wadannan magungunan ka iya cutar da su da kara tabarbarewar lafiya.

''Muhimmin abu ga magani shi ne ya kasance ba mai cutarwa ba.''

Cibiyar binciken cutar kansa da ke Birtaniya, ta wallafa a shafinta na internet, mutane su guji gwama maganin gargajiya da na asibiti matukar su na son ganin tasirinsa.

Haka kuma cibiyar ta bayyana muhimmancin kaucewa wasu nau'o'in abinci, da kayan marmari kamar lemon taba da lemon zaki a lokacin da suke shan magani.

"Fara tuntubar likitanka kan wani abu da kake son fara amfani da shi, abinci, ko kayan lambu ko na marmari a lokacin da ake maka maganin, ta yin hakan za a kaucewa aikata ba daidai ba da zai iya janyo sanadin fadawarka cikin mawuyacin hali."

Yayin taron karawa juna sani kan cutar kansa da aka yi a karo na biyar, Farfesa Cardoso ta ce maganin gargaji da ake yi da sassan jiki misali yoga, suna shafar tasirin maganin da likitoci ke bayarwa a asibiti.