Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi wa dan wasan Manchester City tiyata
Dan kwallon Manchester City, Oleksandr Zinchenko zai yi doguwar jinya bayan da aka yi masa tiyata a gwiwarsa.
Dan wasan, mai shekaru 22, wanda ya murzawa City din kwallo sau bakwai a bana, yana jinya a kasar Spain.
Jinyarsa za ta iya kawo wa City din nakasu, saboda wani dan wasan bayan Aymeric Laporte shi ma zai shafe lokaci mai tsawo yana jinyar rauni.
A yanzu haka dai an maida Rodri ya koma buga baya duk da cewa shi dan tsakiya ne, sai dai kuma shi ma din ya ji rauni a tsakiyar mako kuma watakila ba zai buga wasan City da Aston Villa a ranar Asabar.
Zinchenko ya wallafa hotonsa a shafinsa na Instagram bayan da aka yi masa tiyata a birnin.