'Kaso 90 na matalautan duniya za su zama 'yan Afirka'

    • Marubuci, Pablo Uchoa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Bankin Duniya ya ce an fitar da mutum fiye da biliyan daya da miliyan 100 daga kangin talauci. Wannan ce wata magana da ta yi wa duniya dadin ji a wannan karnin.

A tsakanin shekarun 1990 da 2015, yawan mutanen da ke rayuwa a kan dala 1.90 ko kasa da haka a duniya, ya fado daga biliyan 1.9 zuwa milyan 735.

Hakan na nufin yawan mutanen da ake nufin matalauta ne idan aka yi la'akari da waccan ma'anar ta talauci, ya fado daga kaso 36 zuwa 10 a lokaci guda.

To sai dai batun yaki da talauci babu dai-daito a cikinsa kuma masanin tattalin arzikin da ya fito da tsarin gano talauci ya shaida wa BBC cewa tsare-tsaren cigaba da ake yi "ba sa tarar da matalauta na hakika".

Martin Ravallion, wanda shi ne tsohon darektan bincike sannan kuma babban mataimakin shugaban Bankin Duniya ya ce "tazarar da ke karuwa tsakanin masu shi da marasa shi ita ce babban kalubalen da muke fuskanta wajen yaki da talauci".

Banbancin kasashen duniya

Bankin Duniya ya ce rashin bunkasar tattalin arziki da tafiyar wahainiyar da tattalin arzikin yake yi a baya-bayan nan su ne ke dakile cigaba a wasu kasashe.

A dai-dai lokacin da mutum bilyan daya a China da India suka fice daga ajin matalauta, yawan masu fama da kangin talauci a hamadar Afirka ke karuwa kamar yadda abin yake shekaru 25 da suka gabata.

"A shekaru 10 da suka gabata mun ga yadda duniya ke tafiya ta fuska biyu," in ji Carolina Sánchez-Páramo, darektar tsarin Global Director of the Poverty and Equity Global Practice a Bankin Duniya.

Ta shaida wa BBC cewa dalilan da ya sa talauci ke karuwa da raguwa a yankunan duniya daban-daban su ne guda hudu;

  • Banbancin karuwar tattalin arziki a duniya
  • Bai wa jama'a dama kamar samar da aikin yi
  • Samun damar cin gajiyar kayan more rayuwa
  • Rikice-rikice a fadin duniya

A 2015, rabin matalautan duniya na tsakanin kasashe biyar na duniya ne - India da Nigeria da jamhuriyar dimokradiyyar Congo da Ethiopia da Bangladesh.

Wani hasashe na baya-bayan nan ya nuna Najeriya ce ke neman yi wa kasar India fintinkau wajen yawan mutanen da suka fi talauci, inda suka kasashen biyu suke da matalauta miliyan 100.

Zuwa 2030, ana hasashen mutum 9 a cikin 10 na mutanen da ke rayuwa kasa ko karkashin dala 1.90 a kowacce rana za su kasance a Afirka kudu da hamadar Sahara.

Yadda za a kai ga talakawa

Yaye talauci a 2030 na daya daga cikin muradun majalisar dinkin duniya. To sai dai wani rahoto a watan Yuli ya ce wani hasashe ya nuna cewa kaso shida na alummar duniya za su kasance cikin talauci.

Bankin Duniya na da wani tsari da yake son bi wajen yaye talauci tsakanin al'umma da kaso uku to amma alamu na nuna cewa bai zama lallai a cimma hakan ba.

Mr Ravallion ya ce tsare-tsaren da ake da su a kasa "ba sa aiki yadda ya kamata ga mutane matalauta amma ba su fama da kangin talauci ba."

To sai dai ya amince cewa "ba a kai wa ga mutanen da suka fi kowa talauci".

*Additional reporting by Fernando Duarte