Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Talauci ne ke kawo tashin hankali a Najeriya - Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai alaka tsakanin talauci da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kasar.
"Idan banbanci tsakanin masu kudi da talakawa ya karu, to sai rashin zaman lafiya ma ya karu, " a cewar shugaban, wanda ke magana a ranar bikin cika shekara 20 da kawo karshen mulkin soji a kasar.
Ya kara da cewa: "za mu ta iya fitar da mutum miliyan 100 daga talauci cikin shekara 10 idan aka samu kyakkyawan shugabanci da sanin ya kamata".
Shugaba Buhari, wanda ya fara wa'adi na biyu a karshen watan Mayu, an zabe shi ne bisa alkawarin samar da zaman lafiya da yaki da cin hanci da rashawa.
Sai dai yayin da aka samu raguwar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa, an kuma samu karuwar sace-sacen jama'a da hare-haren 'yan bindiga a wasu sassan kasar.
Shugaban ya kuma ce tun da kasashen China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya cigaba.
Sai dai bai yi wani cikakken bayani kan yadda zai yi hakan ba, abin da ya sa masanin tattalin arziki Abubakar Aliyu ya ce zance ne kawai.
"A yanzu babu wani tsari a kasa da ake da shi da zai nuna cewa hakan mai yiwuwa ne, a don haka ina ganin kalamai ne kawai irin na 'yan siyasa da sukan yi," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Najeriya ta fi kowacce kasa yawan arzikin man fetur da kuma jama'a a Afirka, amma tana sahun gaba-gaba a jerin kasashen da ke fama da rashin ci gaba, abin da ake alakantawa da cin hanci da rashin ingantaccen shugabanci.
Wannan ne karon farko da ake yin bikin Ranar Demokuradiyyar a 12 ga watan Yuni.
An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma "rage radadin" alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993.
Shugaba Buhari ya kuma sanar da sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa Moshood Abiola, mutumin da aka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben na 1993 wanda gwamnatin sojin lokacin ta soke.
Wannan sanarwa dai ita ce ta fi birge wadanda suka halarci wurin taron idan aka yi la'akari da yadda wurin ya kaure da tafi bayan da ya ayyana hakan.
Jawabin Buhari
Shugaba Buhari ya shafe dogon lokaci yana jawabi inda ya bayyana rawar da Najeriya take takawa wurin tabbatar da demokuradiyya da kuma inganta tsaro a nahiyar Afirka.
Sannan ya lissafa abubuwan da ya ce gwamnatinsa ta samar a shekaru hudun da ya yi a kan karagar mulki wadanda suka hada da:
- Inganta harkokin tsaro - ciki har da yaki da Boko Haram - wanda ya ce ya tabarbare a lokacin da ya hau mulki a 2015
- Sai dai ya ce har yanzu akwai sauran aiki domin masu satar mutane da 'yan bindiga na ci gaba da addabar jama'a
- Kowa ya san mun yi nisa a yaki da cin hanci da kuma samar da ayyukan yi
- Gyara kuraren da gwamnatocin baya suka yi
- Bunkasa tattalin arziki da yaki da talauci
- Samar da ayyukan ci gaba da suka hada da gina hanyoyi
Abin da zai mayar da hankali a kai
Duk da cewa shugaban bai ayyana wani takamaiman alkawari ga 'yan kasar ba, amma ya bayyana wasu abubuwa ko fannonin rayuwa da ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hanakali a kai a wa'adin mulkinsa na biyu.
- Dorawa kan ayyukan cigaban da ya ce gwamnatinsa ta samar a fannoni daban daban
- Tabbatar da hadin kan kasar da kuma yi wa kowanne bangare adalci
- Yaki da talauci - za mu iya raba mutum miliyan 100 da talauci idan aka samu kyakkyawan shugabanci
- Inganta harkokin lafiya a matakin kananan hukumomi da gwamnatocin tsakiya
- Tallaffawa masu kananan masana'antu
- Gina kananan hanyoyi domin agazawa 'yan kasuwa da manoma
- Bayar da tallafi ga masu zuba jari
- Kammala gina hanyoyi na tsawon kilomita 2000
Bikin ya samu halartar wasu shugabannin Afirka da suka hada da na Rwanda da Chadi da Nijar da kuma Gambia.
Haka kuma akwai manyan jami'an gwamnati ciki har da sabbin shugabannin majalisun dokoki na tarayya.
Sai dai babu daya daga cikin tsaffin shugabannin kasar da ya halarci taron. Haka kuma babu jami'an babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.