Karshe!
Nan muka kawo karshen karshen labarai da rahotanni kai tsaye game da Ranar Dimokradiyya a Najeriya ta bana. Mun gode.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labarai da rahotanni kai tsaye game da Ranar Dimokradiyya a Najeriya, inda a bana kasar take bikin cika shekara 20 da komawa tafarkin dimokradiyya.
Naziru Mikailu, Umar Rayyan and Umar Mikail
Nan muka kawo karshen karshen labarai da rahotanni kai tsaye game da Ranar Dimokradiyya a Najeriya ta bana. Mun gode.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu abin da zai hana kasar ci gaba kamar kasashen China da India ko Indonesia.
"Tun da China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya ci gaba," a cewar shugaban, wanda aka sake zaba karo na biyu a watan Fabrerun da ya gabata.
Ya kara da cewa: "Kasashen China da Indonesia sun ci gaba karkashin tsarin mulkin mulukiya yayin da India ta kai gaci a karkashin tsarin demokuradiyya, a don haka muma babu abin da zai hana mu mu kai ga gaci".
Shugaban na magana ne a ranar bikin murnar demokuradiyya, wacce a karon farko ake tunawa da ita a ranar 12 ga watan Yuni.
An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma rage radadin alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993.
Shugaba Buhari ya kuma sanar da sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa Moshood Abiola, mutumin da aka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben na 1993 wanda gwamnatin sojin lokacin ta soke.
Wannan sanarwa dai ita ce ta fi birge wadanda suka halarci wurin taron idan aka yi la'akari da yadda wurin ya kaure da tafi bayan da ya ayyana hakan.
Teburin manyan baki kenan ciki har da shugaban kasar Rwanda (na farko daga hagu).
Karewar jawabin Shugaba Muhammadu na nufin an kawo karshen wannan taro na bikin dimokradiyyar Najeriya 'yar shekara 20 ba tare da katsewa ba.
Yanzu haka fareti ne sojoji ke yi yayin da su kuma manyan baki ke ficewa daga filin taron.
Daga hagu zuwa dama, Aisha Buhari uwar gidan shugaban kasa da Sanata Ahemd Lawan Shugaban Majalsiar Dattawa da Femi Gbajabiamila Kakakin Majalsar Wakilai da Bola Ahmed Tinubu jagoran jam'iyyar APC mai mulki yayin da ake rera taken Najeriya.
Shugaba Buhari ya gama jawabinsa, inda aka yi taken Najeriya.
Yanzu za a ci gaba da faretin girmamawa ga manyan baki.
"Daga yau na mayar da sunan babban filin wasa na kasa da ke Abuja Moshood Abiola National Stadium" - Buhari
"Wannan gwamnati ba za ta yadda da aikin duk wanda yake so ya tsokani ko yi wa al'adunmu ba'a ba ko kuma ya kawo wa tsaron kasa cikas" - Buhari
"Ina mika godiya ta musamman ga 'yan kasuwa wadanda suka gina wuraren kasuwanci kamar layukan wayar hannu da kuma sauran wurare wadanda suka bai wa matasanmu aikin yi" - Buhari
"A matsayina na shugaban komitin farfado da tafkin Chadi zan jagoranci zama na musamman don kawo karshen matsalolin tsaro a yankin" - Buhari
"Shirye-shiryenmu na habbaka rayuwar 'yan kasa (N-power da ciyar da 'yan makaranta) abin koyi ga sauran kasashen duniya" - Buhari
"Ba mu tsorata da kalubalen da ke gabanmu ba sai dai ma sun kara mana kwarin gwiwa ne" - Buhari
"Bambancin 2015 da 2019 dangane da harkar tsaro shi ne cewa a wannan karo muna yin aiki tare da jam'ian tsaro masu yawa da bayanan sirri da kuma kayan aiki," Buhari ya fada
Shugaba Muhammadu Buhari ya fara gabatar da jawabinsa, wanda dama shi ne babban abin da za a yi a yau.
Za ku iya garzayawa shafinmu na BBC Hausa Facebook don kallon bidiyon wainar da ake toyawa kai-tsaye a dandalin Eagle Square wato inda ake bikin cika shekara 20 da komawa tafarkin dimokradiyya a Najeriya ranar Laraba.
An fara fareti a dandalin Eagle Square bayan isowar Shugaba Buhari.
Shugaba Buhari lokacin da yake kewaye dandalin Eagle Square.