Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mahaifina bai kanainaye gwamnatin Buhari ba —Fatima Mamman Daura
Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron hirar Yusuf Yakasai da Fatima Mamman Daura:
Fatima Mamman Daura, 'yar makusancin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce mahaifinta bai kanainaye gwamnatin Buhari ba kamar yadda wasu ke tunani.
A hirarta da BBC, Fatima ta ce mahaifinta Mamman Daura da Shugaba Buhari sun tashi tare kuma abokansu daya don haka ne ya sa kusancinsu ya yi yawa.
Ta ce "kowa na da amini, wanda yake jin maganarsa. To aminan juna ne sosai, shi ya sa mutane ke ganin kamar ya kankane gwamnatin."
Mamman Daura dan uwa ne na kusa ga shugaban Najeriyar - Buhari kawunsa ne - kuma duk da cewa ba shi da mukami a gwamnatin amma ana hasashen cewa yana da fada-a-ji a fadar ta shugaban kasa.
Fatima ta ce ba gaskiya ne ba zancen da ake cewa mahaifinta ya kanainaye Shugaba Buharin sai yadda ya ce ake yi, "Baba mutum ne mai kawaici, ba ya son shiga ma harkar mutane kuma bai cika yawan magana ba, kuna ma iya yin bincike akai ku gani," a cewar Fatima.
"Na san shugaban kasa kan nemi shawararsa ammaidan ya ba da shwarar ya kan janye ne ba ya katsalandan, yana gidan yana tasbihinsa, ko mun masa maganar cewa yake mu daina damuwa ana kankare masa zunubi ne.
Ta ci gaba da cewa "ba ma jin dadin abin da ake fada a kansa amma dai mun san kasancewar sy tare ne ya sa ake masa haka albarkanci zumunci."
Sharhi, daga Halima Umar Saleh
An dade ana ce-ce-ku-ce a Najeriya a kan wannan batu, musamman tun bayan da Shugaba Buharin ya bai wa Mamman Daura da iyalansa damar tarewa a wani gida da ake kira Glass House a cikin fadar shugaban kasar.
Sai dai shekaru biyu da suka gabata rahotanni sun ce Shugaban na Najeriya ya nemi Malam Mamman da ya fita daga Glass House ya koma wani gidan wanda shi ma yake cikin fadar, domin dan shugaban wato Yusuf Buhari ya zauna ya yi jinya bayan hatsarin da ya yi.
'Yan Najeriya sun dade suna guna-guni a kan zaman Mamman Daura a fadar gwamnatin kasar, al'amarin da suke ganin kamar yana bai wa dan uwan shugaban damar yin katsalandan a cikin al'amuran gwamnati, "duk da cewa ba shi da wani mukami kuma ba shi aka zaba ba."
Sai dai wasu da dama na ganin zaman Mamman Daura a fadar shugaban kasa ba wani abu ba ne, idan aka yi la'akari da kusancin su tuntuni, da kuma "irin goma ta arzikin da ya yi wa Buharin a lokutan baya."
A daya bangaren kuma, ana ganin kamar Mamman Daura ne yake hana Aisha Buhari rawar gaban hantsi a matsayinta na uwargidan shugaban kasar.
Sai dai duk da cewa ba ta taba fitowa fili ta ambaci sunansa ba, ta sha yin shagube game da wasu da take kira makusantan mijinta wadanda take cewa sun kanainaye al'amuran gwamnati, lamarin da wasu ke ganin tamkar sukar mijin nata take yi kai tsaye.
Duk wadannan abubuwa da ke faruwa dai ba a taba jin ta-bakin Shugaba Buhari ko shi Mamman Daura ba.
A watan Yunin 2019 dai 'yan Najeriya suka sako gwamnatin Shugaba Buhari a gaba a shafukan sada zumunta da kiraye-kirayen a kori wasu na kusa da shi, wanda suka hada da Mamman Daura.
Hakan ya biyo bayan wata zanga-zangar da wasu matasan jam'iyyar APC mai mulki suka yi ne a kan batun.
Sai dai a lokacin, mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya gaya wa BBC cewa wasu masu neman mukami ne suka debo mutane su yi zanga-zangar.
"Wadansu sun sa ido a kan wadannan mukamai saboda wasu bukatu nasu," in ji shi.
Karin labaran da za ku so ku karanta