Hotuna: Rigar Aisha Buhari ta bar baya da kura, sabon zubi a majalisar Najeriya

A kwana a tashi ba wahala, ga shi har mako ya zo karshe.

Sai dai a Najeriya, wannan makon daga 8 ga watan Yuni zuwa 14 ga wata mai dumbin tarihi ne da ba za a manta da shi ba, saboda faruwar al'amura masu muhimmanci.

Daga cikin abubuwan da suka ja hankalin jama'a har da shigar da matar shugaban kasar Aisha Buhari ta yi a wajen liyafar cin abincin dare da aka shirya don bikin ranar dimokradiyya, inda ta saka wata riga ta naira miliyan 1.5.

Ga dai wasu zababbun hotuna na abubuwan da suka faru a kasar ko ga wasu 'yan kasar a wasu kasashen...