A kwana a tashi ba wahala, ga shi har mako ya zo karshe.
Sai dai a Najeriya, wannan makon daga 8 ga watan Yuni zuwa 14 ga wata mai dumbin tarihi ne da ba za a manta da shi ba, saboda faruwar al'amura masu muhimmanci.
Daga cikin abubuwan da suka ja hankalin jama'a har da shigar da matar shugaban kasar Aisha Buhari ta yi a wajen liyafar cin abincin dare da aka shirya don bikin ranar dimokradiyya, inda ta saka wata riga ta naira miliyan 1.5.
Ga dai wasu zababbun hotuna na abubuwan da suka faru a kasar ko ga wasu 'yan kasar a wasu kasashen...
Asalin hoton, Daily Trust
Bayanan hoto, A farkon mako ne Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kai wa sarkin Kano Muhammadu Sunusina II ziyara jim kadan bayan dawowarsa daga Umrah.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wata mata mai sayar da kifi a unguwar Agege ta birnin Ikko a jihar Legas tana bacci a ranar Litinin. Duk da cewa an haramta sayar da abu a bakin titi, ita ce hanyar mafi yawan mutane ta samun kudi daga sana'o'insu.
Asalin hoton, Buhari Sallau
Bayanan hoto, A wannan ranar ne dai kuma dakarun bataliya ta 121 ta rundunar sojojin Najeriya ta ceto wasu mata da yara daga mayakan Boko Haram tare da hadin gwiwar mafarauta a wani kwanton bauna da suka ka yi wa mayakan a kauyen Gwadalana na jihar Borno.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Talata kuwa ta kasance ranar da aka kaddamar da majalisar dokokin Najeriya zubi na tara. A nan wasu 'yan majalisar dattawa mata ne suke kada kuri'ar zaben shugabannin majalisar ......
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ......Bayan kammala kada kuri'un nasu dai Sanata Ahmed Lawan ne ya samu nasarar zama shugaban majalisar dattawan, inda ya doke abokin takararsa Sanata Ali Ndume.
Asalin hoton, Aisha Buhari Facebook
Bayanan hoto, A wannan rana ne dai kuma uwar gidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari tare da matan shugabannin kasar Ghana da Nijar da Chadi da Gambia suka yi wani taro a Yola....
Asalin hoton, LuciPost
Bayanan hoto, ..... A daren ranar Talata din ne kuma Aisha Buhari ta halarci liyafar dare da shugaban kasa ya shirya albarkacin Ranar Damokuradiyya ta Najeriya. An ga Hajiya Aisha sanye da wata bakar riga mai surfani wacce ta jawo ce-ce-ku-ce a kasar, inda aka kiyasta kudinta a kan kusan naira miliyan 1.6. 'Yan Najeriya dai sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan shiga.
Asalin hoton, Twitter/NuhuIbrahim
Bayanan hoto, Farfesa Ibrahim Garba kenan a ranar Talata yayin da yake bai wa Nuhu Ibrahim lambar girmamawa bayan ya lashe wata gasar komfuta da aka shirya tsakanin jami'o'in Najeriya.
Asalin hoton, Twitter/NuhuIbrahim
Bayanan hoto, An shirya gasar ne tsakanin jami'o'i 16 na gwamnati da masu zaman kansu, inda Nuhu ya wakilci jami'ar Ahmadu Bello.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, An wayi garin Laraba da bikin Ranar Damokuradiyya ta kasar. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a lokacin da ake tuka shi a mota, inda yake duban masu faretin girmamawa a Dandalin Eagle Square.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ... Shugabannin kasashe kusan hudu ne suka halarci taron ciki har da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, wanda shi ne na gaba a hoton nan a yayin isarsa Dandalin Eagle Square.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ranar Larabar ba ta kare ba sai da tawagar 'yan wasan kwallon kafa ta mata ta Najeriya Super Falcons suka lallasa takwarorinsu na Koriya Ta Kudu a Gasar Cin Kofin Duniya ta mata da ake yi a Faransa.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Kocin Super Falcons Thomas Dennerby, yana murnar nasarar da tawagar tasa ta samu.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar ne dai kuma wasu 'yan Najeriya Bilikiss da Olawale Adebiyi suka karbi kyautar King Baudouin ta Ci gaban Afirka a birnin Brussels na Belgium.
Asalin hoton, Aisha Buhari Facebook
Bayanan hoto, Ranar Alhamis kuwa an sake ganin Aisha Buhari da irin rigar da ta sanya ranar Talata a wajen wata liyafa da ta shirya don bankwana da matan gwamnonin da ba za su dawo ba.
Asalin hoton, Aisha Buhari
Bayanan hoto, Liyafar bankwana da matan gwamnonin ta tara mutane da dama daga sassa daban-daban na kasar.