Ko kun san tafiya a hankali na janyo 'saurin tsufa'?

    • Marubuci, Philippa Roxby
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health reporter, BBC News

Irin yadda mutane ke tafiya a lokacin da suka haura shekaru 40 alama ce da ke nuna irin yadda kwakwalwarsu da kuma jikinsu ke tsufa, kamar yadda masu binciken kimiyya su ka gano.

Masanan sun yi amfani ne da wata manhaja da ke nuna yadda matakan tsufa su ke.

Ba kawai jikin masu tafiya a hankali ke nuna saurin tsufa ba,hatta fuskokinsu kan takure kuma da ma suna da karamar kwakwalwa.

Kungiyar ta kasa da kasa da ta gudanar da wannan bincike ta bayyana matukar mamaki kan abin da ta gano.

Mafi yawancin loikitoci kan yi amfani da manhajar 'gait speed' domin duba lafiyar jama'a musamman tsofaffi da suka haura shekaru 65,wurin gano karfin jijiyoyinsu da lafiyar huhunsu da kashin baya da kuma idonsu.

Bugu da kari, tafiya a hankali ga tsofaffi na da alaka da cutar mantuwa.

Binciken ya yi amfani da mutane 1,000 a New Zealand da aka haifa a shekarar 1970, inda aka gudanar da bincike kan yanayin jikinsu da kwakwalwarsu tare da yin gwaji kan yadda suke fahimtar abubuwa duk bayan wasu shekaru tun a lokacin kurciyarsu.

Binciken dai ya tabbatar da cewa tafiya a hankali alama ce ta wata cuta da ta dade a jikin mutun wadda kuma ta kama shi ne shekaru da dama kafin tsufansa, a cewar Prof Terrie E Moffitt,wanda ke jagorantar binciken daga Jami'ar King's College London da kuma Jami'ar Duke da ke Amurka.

Ko a shekaru 45 akwai bambanci sosai bayan lura da cewa masu tafiya da sauri kan yi tafiyar mita biyu a cikin dakika daya ba tare da sun yi sassheka ba.

A takaice, masu tafiya a hankali sun nuna alamun 'tsufa da wuri' yayin da huhunsu da hakoransu da kuma kwayoyin halittarsu ke samun nakasu ba kamar na sauran takwarorinsu ba da ke tafiya da sauri.

Bayan zurfafa bincike an kuma gano cewa kwalkwalwar masu tafiya a hankali kan tsufa da wuri.

Kuma masu binciken sun yi nasarar gano yanayin saurin tafiyar masu shekaru 45 ta yin amfani da manhajoji daban-daban tun suna da shekaru uku.

Hakan ya nuna cewa kananan yara da ke girma da matsalar tafiya a hankali na da nakasun karfin kwakwalwa da kashi 12 idan aka kwatanta da takwarorinsu da ke tafiya da sauri bayan sun shekara 40 ko fiye da haka.

Alakar tafiya a hankali da tsarin rayuwa

Sai dai wata kungiyar masu bincike ta gano cewa bambancin lafiya da karfin kwakwalwa na da alaka da irin yadda yara ke samun kula da lafiya tun bayan haihuwarsu.

Sun kuma bayyana cewa tun a lokacin za a iya fahimtar wanda zai iya tsufa da cikakkar lafiya.

Gano irin saurin da jama'a ke yi a lokacin da suke tafiya tun lokacin kuruciyarsu ita ce babbar hanyar magance wannan matsala.

Akwai wasu hanyoyin kawar da wannan cuta da suka hada da cin abinci maras kitse sosai, da kuma amfani da kwayar 'metformin' duk da ba a kammala bincike maganin ba.

Akwai kuma bukatar jama'a su kula da lafiyar kwakwalwa da kuma ta jiki tare da sauya yanayin tsarin rayuwarsu tun suna da kuruciya da cikakkar lafiyar yin hakan.